Bayan Taso Shi a Gaba, Gwamna Lawal Ya Tsage Gaskiya kan Jita Jitar Barin PDP
- Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya karyata jita-jitar barin PDP, yana cewa labaran karya ne da ba su da tushe ko makama
- A wani rubutu da ya wallafa a Facebook, Gwamna Lawal ya bayyana cewa shi cikakken ɗan jam'iyyar PDP ne kuma bai da niyyar canza jam’iyya
- Gwamnan ya ce wasu ke yaɗa jita-jitar domin su ɓata masa suna da kawar hankalin jama'a daga nasarorin da yake samu a Zamfara
- Ya bukaci jama’a su yi watsi da makirci, yana mai cewa kokarinsa na ceton jihar Zamfara ba zai tsaya ba saboda kage
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi magana kan jita-jitar barin jam'iyyar PDP.
Gwamna Dauda Lawal ya yi watsi da karairayi da ake yaɗawa cewa yana shirin barin jam'iyyar PDP zuwa wata.

Asali: Twitter
Wanann na kunshe ne a cikin wani rubutu da Gwamna Lawal ya yi a yau Lahadi 20 ga watan Afrilun 2025 a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya koka kan tulin basuka a Zamfara
Wannan na zuwa ne bayan Dauda Lawal ya koka kan yadda ya samo jihar Zamfara bayan karɓar mulki a hannun Bello Matawalle.
Gwamna Dauda ya koka kan tarin matsalolin da ya gada wajen magabacinsa, Bello Matawalle inda ya ce abin takaici ne.
Dauda Lawal ya bayyana cewa N4m kawai aka bar masa a asusun jihar, sai kuma tarin basussuka na biliyoyin naira.
Gwamnan ya nuna cewa hakan ne ya sanya ya duƙufa wajen aiki tuƙuru domin warware matsalolin da ya tarar.

Asali: Facebook
Dauda Lawal ya yi magana kan barin PDP
A cikin sanarwar, Gwamna Dauda ya yi fatali da rade-radin inda ya ce shi cikakken dan jam'iyyar PDP ne.
Ya bukaci al'umma su yi watsi da masu neman yada karya domin cimma wani buri da suka sanya a gaba.
Sanarwar ta ce:
"Ni Dauda Lawal, cikakken ɗan jam'iyyar PDP ne.
"Ku yi watsi da labarun ƙarya na cewa wai zan koma wata jam'iyya."
Waɗanda Dauda Lawal ke zargi da jita-jita
Gwamna Dauda Lawal ya ce hakan wani salo ne da wasu magauta ke yi domin dauke hankulan mutane daga abubuwan ci gaba da yake yi a Zamfara.
Ya kara da cewa:
"Wannan wani salo ne na magauta kuma 'yan basaja don su ɗauke hankalinmu daga ƙoƙarin da muke yi na ceton jihar Zamfara."
Wani ɗan PDP kuma masoyin Dauda Lawal a Gombe ya zanta da Legit Hausa kan matsayar gwamnan.
Kwamred Aliyu Abdulkadir ya ce daman zai yi wahala Dauda Lawal ya butulcewa PDP kamar sauran gwamnoninta.
"Dauda Lawal ɗan amana ne kuma wanda zai yi wahala ya ci amanar PDP ba kamar sauran gwamnoni ba."
- Cewar Aliyu
Ya shawarci sauran gwamnoni su yi tunani kafin matakin barin jam'iyyar da ya yi musu gata.
Ana zargin Gwamnonin PDP za su koma APC
Kun ji cewa wasu rahotanni sun gwamnoni uku na PDP na shirin sauya sheka zuwa APC, domin marawa shugaba Tinubu baya a yunkurinsa na zarcewa a 2027.
Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa babu jam'iyya a Akwa Ibom yanzu, suna aiki tare da APC domin hadin kai da ci gaban kasa.
Gwamna Oborevwori, Mbah da Fubara suna nazarin marawa Tinubu baya ba tare da sauya sheka ba, yayin da wasu ke tattaunawa kan sauyin jam’iyya.
Asali: Legit.ng