Sarakunan Arewa Sama da 86 Sun Yi Magana da Murya Daya kan Tsaro

Sarakunan Arewa Sama da 86 Sun Yi Magana da Murya Daya kan Tsaro

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce sarakunan gargajiya sun fi damuwa da rikice-rikicen tsaro fiye da ‘yan siyasa
  • Ya ce lokaci ya yi da za su hada kai a matsayin ‘yan uwan juna a ce ya isa haka game da kashe-kashen da ke faruwa a Arewa da Nijeriya baki ɗaya
  • Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kira da a hada karfi tsakanin gwamnoni, shugabannin addinai da al’umma domin dakile matsalar tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya a Nijeriya sun fi damuwa da rashin tsaro fiye da ‘yan siyasa.

Sarkin ya bayyana haka ne a taron kwamitin zartarwan Majalisar Sarakunan Gargajiyan Arewa karo na bakwai da aka gudanar a Maiduguri, jihar Borno, ranar Talata 15 ga Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

Portable: Ƴan sanda sun kama fitaccen mawakin Najeriya, an ji laifin da ya aikata

Sarakuna
Sultan ya bukaci hada kai domin tunkarar matsalar tsaro. Hoto: @NTANewsNow
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce sun shirya zama domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa sun kuduri aniyar fitar da matsaya guda da za ta fitar da yankin daga halin da ake ciki.

An bukaci kawo karshen kashe kashe a Arewa

Sarkin Musulmi ya ce sarakuna sama da 86 da ke da mukamai daban-daban sun yi magana da murya daya sun ce 'ya isa haka' dangane da kashe-kashen da ake yi a Arewa da kasa baki daya.

A cewarsa:

“Mun fitar da bayanai da yawa na Allah wadai.
"Amma har yaushe za mu ci gaba da yin hakan kafin ‘yan siyasa da hukumomin tsaro su dauki matakin da zai rage ko kawo karshen matsalolin tsaro a kasar nan?”

Sarkin ya jaddada cewa ba za su gaza ba wajen fadakar da shugabanni da kuma bayar da shawara don a samu zaman lafiya da kare rayukan al’umma.

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan kisan ɗan bindiga, miyagu sun ɗauki fansa, sun ƙona masallacin Juma'a

Sarakuna za su taimaka wa gwamnoni

Sarkin Musulmi ya bayyana cewa sarakunan gargajiya ba sa neman mukamin siyasa, amma suna neman a ba su dama su taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaro.

Ya ce:

“Ba mu gasa da gwamnoni, muna dai taimaka musu ne."

Ya ce suna sa ran Allah zai basu ikon kawo karshen Boko Haram da sauran masu tada kayar baya, yana mai cewa dole ne a nuna zumunci da haɗin kai a tsakanin 'yan Arewa.

Sarkin ya kammala da cewa duk da matsalolin tsaro a Najeriya, akwai kasashen da ake kashe mutane fiye da yadda ake kashe su a kasar nan.

A karkashin haka ya jaddada bukatar dogaro ga Allah da ci gaba da neman zaman lafiya a fadin Najeriya.

Sultan
Sarkin Musulmi ya bukaci kawo karshen matsalar tsaro a Arewa. Hoto: National Moon Sighting Committee
Asali: Facebook

An kafa dokoki a Filato kan hare hare

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Filato ta dauki matakan dakile kai hare haren 'yan bindiga da ake ta fama da su.

Kara karanta wannan

Yadda riƙaƙƙen ɗan bindiga ke bautar da jama'a, ya yi musu barazanar noma

Mai girma Gwamna Caleb Mutfwang ya tabbatar da kafa sababbin dokoki domin hana faruwar kai hare hare kan al'umma.

Mutfwang ya kuma bayyana cewa za a ba wadanda aka jikkata a hare haren jihar kulawar lafiya kyauta a dukkan asibitocin Filato.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng