'Sun San Komai,' 'Dan Majalisa Ya Dauki Zafi bayan Hare Hare a Filato

'Sun San Komai,' 'Dan Majalisa Ya Dauki Zafi bayan Hare Hare a Filato

  • 'Dan majalisa mai wakiltar Bassa/Jos ta Arewa a majalisar wakilai, Daniel Asama, ya zargi jami’an tsaro da cewa suna da bayanai game da masu kai hari Filato
  • Asama ya bayyana cewa kisan gillar da ake ci gaba da yi a wasu sassan Filato na da kamanceceniya da yunkurin karbe ƙasa daga hannun mutanen yankin
  • Zuwa yanzu, mutane kimanin 100 ne suka rasa rayukansu cikin makonni biyu sakamakon hare-haren da ba su lafa ba a jihar, wasu da dama sun rasa muhalli
  • Hon. Asama ya ce akwai bukatar jami’an tsaro su yi amfani da bayanan da mutanen yankin za su iya bayarwa wajen kawo karshen kisan gilla da ake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – 'Dan majalisa mai wakiltar mazabar Bassa/Jos ta Arewa a majalisar wakilai, Hon. Daniel Asama, ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-hare ke ci gaba da karuwa a jihar Filato.

Ya ce jami’an tsaro suna da masaniya game da wuraren da wadanda ke da hannu a kisan gillar da ake yi a jihar ke fakewa, yana mai kiran hare-haren da cewa na kisan kare dangi ne.

Caleb
Dan majalisa ya caccaki jami'an tsaro a kan harin Filato Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Tashar Channels ta ruwaito cewa sama da mutane 100 ne suka rasa rayukansu cikin makonni biyu a jihar Filato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisar ya bayyana kisan a matsayin mummunan lamari da ke bukatar a dauki matakin gaggawa don kawo karshen matsalar.

'Dan majalisar Tarayya ya fusata da harin Filato

Hon. Asama ya jaddada cewa jami’an tsaro suna da cikakken bayani kan inda hare-haren ke tasowa da kuma hanyar da ‘yan ta’addan ke bi.

Ya ce:

"Jami’an tsaro sun san inda wadannan hare-hare ke fitowa. Sun san hanyar da hare-haren ke tasowa."

Harin Filato: Dan majalisa ya shawarci jami’an tsaro

'Dan majalisar ya kara da cewa al’ummar yankin da abin ya shafa za su iya nuna hanyoyin da ake bi wajen kai masu hare-haren.

Sannan yana ganin za su iya taimakawa jami'an tsaro da karin bayani da zai taimaka masu wajen dakile matsalar.

Caleb
Gwamnan Filato, Caleb Muftwang Hoto: Caleb Muftwang
Asali: Facebook

Hon. Asama ya ce:

"Idan jami’an tsaro suka tattauna da mutane, za su gane inda masu hare-haren ke fitowa. Ban yarda da cewa ba su san inda wadannan mutane ke fitowa ba."

Ya bayyana cewa kisan da ake yi ya haddasa raba mutane da muhallansu, yana mai cewa abin da ke faruwa ya kama da yunƙurin karbe ƙasa daga hannun al’umma.

Asama ya bayar da shawara cewa lokaci ya yi da za a dauki matakin kawo karshen kashe kashen, da kuma dawo da zaman lafiya garuruwan.

'Yan sanda sun kama wasu a Filato

A wani labarin, kun ji cewa Sufeto Janar 'yan Sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya sake nuna damuwa game da hare-haren kisan gillar da ke ci gaba da afkuwa a jihar Filato.

Wannan na zuwa ne yayin da Sufeto Janar ya kai ziyara ta musamman a Filato a ranar Talata, 15 ga Afrilu, 2025, domin jajantawa da kuma duba halin da ake ciki bayan kisan bayin Allah.

Sanarwar ta ce wadanda aka kama sun fara bayar da hadin kai ta hanyar bayyana bayanai masu amfani da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen gano sauran da ke da hannu a harin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.