Rashin Tsaro: Atiku Ya Bukaci Sanya Dokar Ta Baci a kan Mulkin Tinubu
- Atiku Abubakar ya soki tafiyar Shugaba Bola Tinubu zuwa Faransa, yana cewa hakan raina hankalin 'yan kasa da ke cikin mawuyacin hali ne
- Ya ce Najeriya na fuskantar gagarumin rikicin tsaro da tattali, yana mai tambayar dalilin da yasa Tinubu ke yawo kasashen waje a irin wannan lokaci
- Atiku ya bukaci Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a kan gwamnatinsa da ya bayyana a matsayin mai cike da gazawa da sakaci kan lamura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fito fili yana sukar tafiyar Bola Ahmed Tinubu kasar Faransa a yayin da kasar ke fama da kalubale masu tarin yawa.
A cikin sanarwar da ofishin yada labaran Atiku ya fitar a ranar 16 ga Afrilu, an bayyana tafiyar Tinubu a matsayin wata hanya ta gujewa daukar nauyin mulki da raina hankalin 'yan Najeriya.

Asali: Getty Images
Sanarwar, wacce Paul Ibe ya fitar a X, ta ce Najeriya na cikin wani hali na matsanancin rikici, da ya kamata shugaban kasa ya maida hankali a kai ba yawo kasashen waje ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Najeriya na fuskantar babban rikici,' Atiku
A cewar Atiku, har zuwa lokacin da Tinubu zai dawo daga tafiyarsa ta baya-bayan nan, zai kasance ya kwashe kwanaki 59 a kasar Faransa tun bayan hawansa kan mulki a Mayun 2023.
Ya bayyana cewa a halin da ake ciki, jihar Filato ta koma filin yaki, inda aka rasa rayukan mutane sama da 100 cikin ‘yan kwanaki , yayin da hare-hare ke ci gaba da addabar Benue da wasu jihohi.
A karkashin haka, Atiku ya yi zargin cewa Tinubu ba ya nuna tausayi ko damuwa da halin da 'yan kasa ke ciki.
Maganar dokar ta-baci a mulkin Tinubu
Atiku ya bayyana tafiyar Tinubu a matsayin wata hanya ta hutu kawai, yana mai cewa babu abin da shugaban kasa ke yi a Faransa da ba zai iya yi a Najeriya ba.
Sanarwar ta ce:
“Wannan ba wata ziyara ce ta jinya ba kamar yadda fadarsa ta fada, amma me zai hana ya zauna a Najeriya ya tunkari matsalolin da suka addabi kasar?”
Atiku ya kalubalanci Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a kan mulkinsa da ya ce ya gaza cika alkawurran da ya dauka na farfado da tattalin arziki da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Asali: Depositphotos
'Tinubu zai gurgunta kasa' inji Atiku
Atiku ya kara da cewa mulkin Tinubu na kara jefa Najeriya cikin halin kunci, inda miliyoyin mutane ke kara fadawa cikin talauci da fargaba saboda rashin tsaro da hauhawar farashi.
Ya bukaci shugaban kasa da ya duba kundin tsarin mulki da ke nuna cewa kare rayuka da walwalar ‘yan kasa shi ne babban aikin gwamnati, yana mai cewa:
“Akwai hadari idan shugaba ba ya jin zafin halin da al’ummarsa ke ciki.”
Sanarwar ta kare da tambaya da cewa:
“Idan Tinubu zai iya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas don dalilan siyasa, me zai hana ya ayyana ta a kan mulkinsa da ke dab da rugujewa?”
Za a yi gangamin goyon bayan Tinubu a Abia
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar matasa a Kudu maso Gabashin Najeriya ta bayyana goyon bayanta ga Bola Tinubu.
Kungiyar ta bayyana shirin nuna goyon baya da yin gangamin matasa miliyan 5 a jihohin Kudu maso Gabas.
Baya ga haka, kungiyar ta jaddada cewa za ta nuna goyon baya ga Sanata Orji Kalu saboda ayyukan da yake yi a jihar Abia.
Asali: Legit.ng