'Yan Ta'adda Sun Farmaki Turakun Wutar Lantarki, Jihohi 2 Sun Fada cikin Duhu
- An lalata turakun wutar lantarki huɗu a tashar Owerri-Ahoada, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a jihohin Bayelsa da Rivers
- Hukumar TCN ta ce injiniyoyinta sun fara tantance barnar da aka yi, tare da shirin gyara turakun don dawo da wutar lantarki a jihohin biyu
- A baya, mazauna Bayelsa sun shafe watanni huɗu cikin duhu saboda irin wannan matsala, wanda ya haddasa masu wahalhalu da tsadar rayuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Mazauna jihohin Bayelsa da Rivers sun fada cikin duhu sakamakon lalata turakun wutar lantarki guda huɗu a tashar wutar Owerri-Ahoada, mai karfin 132kv.
Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, TCN ta bayyana cewa an lalata turaku huɗu a kan wannan layin, lamarin da ya haifar da lalacewar wutar gaba ɗaya.

Asali: Getty Images
'Yan ta'adda sun lalata turakun wutar lantarki
Kakakin TCN, Ndidi Mbah, ta ce an lalata turakun T171 zuwa T174, wanda ya haddasa lalacewarsu da misalin ƙarfe 6:23 na yammacin Talata, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa lalata turakun ne ya haifar da wannan matsala, kuma ƙoƙarin sake haɗa wutar bai yi nasara ba.
Wannan matsala ta haifar da katsewar wutar lantarki a tashoshin rarraba wuta na Ahoda, Gbarain, da Yenagoa, wanda ya shafi sassan jihar Rivers da Bayelsa gaba daya.
Ma'aikatan TCN na kokarin gyara wutar
A cewar Mbah, wata tawagar injiniyoyi ƙarƙashin jagorancin babban manajan yankin Fatakwal, Emmanuel Akpa, sun ziyarci wurin don tantance girman barnar da aka yi.
Akpa ya ce hukumar TCN na bakin ƙoƙari don tara ma’aikata da kayan aiki domin gyara lalatattun turakun tare da dawo da wutar lantarki a yankunan da matsalar ta shafa.
“Muna Allah wadai da wannan danyen aiki, wanda ke ktse samar da ingantacciyar hanyar isar da wutar lantarki ga wadannan yankuna,” in ji Mbah.

Kara karanta wannan
'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu
Vanguard ta rahoto cewa, ya kuma yi kira ga al’ummomin da ke kewaye da wadannan turakun su taimaka wajen hana irin wannan mummunan ta'addi a kan kayayyakin wutar lantarki.
Bayelsa, Rivers sun shafe wata 4 a duhu

Asali: Facebook
A baya, mazauna jihar Bayelsa sun sha fama da rashin wutar lantarki har tsawon watanni huɗu daga watan Yuli 2024, sakamakon irin wannan aika-aika.
Rashin wutar lantarki ya jefa jama’a cikin ƙuncin rayuwa, inda yawanci suka dogara da janareta don samun haske da gudanar da ayyukan su na yau da kullum.
Wasu 'yan kasuwa sun ce dole suka rika kashe makudan kuɗi don siyan fetur domin tayar da janaretoci, wanda ya ƙara musu wahalhalun rayuwa.
Hukumar TCN ta sake jaddada cewa tana aiki tukuru domin ganin an dawo da wutar lantarki ga waɗanda lamarin ya shafa cikin gaggawa.
Tushen wutar lantarkin Najeriya ya samu matsala
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tushen wutar lantarki ta ƙasa ta fuskanci matsala, wanda ya haddasa katsewar wuta a sassan Najeriya, musamman a jihar Legas.
Duk da ikirarin gwamnati na kai matakin samar da wutar lantarki zuwa megawatt 6,000, rahotanni sun bayyana cewa adadin ya ragu zuwa ƙasa da megawatt 1,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng