Sabuwar Matsala: Najeriya Ta Rage Yawan Lantarkin da Ake Aikawa Kasar Nijar

Sabuwar Matsala: Najeriya Ta Rage Yawan Lantarkin da Ake Aikawa Kasar Nijar

  • Najeriya ta rage yawan wutar lantarkin da take sayar wa Jamhuriyar Nijar daga megawatt 80 zuwa 46, wanda ke nuna raguwar kusan 42%
  • Ministar makamashin Nijar ta ce matakin ya sa kamfanin lantarki na Nigelec ke dauke wuta har na kwanaki a birnin Niamey da kewaye
  • Najeriya da kanta na fama da karancin wuta sakamakon rashin isasshen gas da kuma dimbin bashin da kamfanonin samar da wuta ke bi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Najeriya ta rage yawan wutar lantarkin da take fitarwa zuwa Jamhuriyar Nijar daga megawatt 80 zuwa megawatt 46.

Najeriya ta dauki matakin ne yayin da ake cigaba da samun rashin jituwa tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar da aka yi juyin mulki.

Kara karanta wannan

Sarakunan Arewa sama da 86 sun yi magana da murya daya kan tsaro

Tinubu
Najeriya ta rage wutar da ta ke ba Nijar. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Image
Asali: Facebook

Bisa wani rahoto da Channels TV ta wallafa a ranar Litinin, 15 ga Afrilu, 2025, matakin ya fara jawo matsalar lantarki a Nijar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa aka rage wutar da ake ba Nijar?

Rahoton ya ce rage adadin wutar na da nasaba da takunkumin da Najeriya da kasashen ECOWAS suka sanya kan gwamnatin sojin Nijar da ta kifar da zababbiyar gwamnati a watan Yulin 2023.

Ministar makamashi ta Nijar, Haoua Amadou, ta ce matakin ya haifar da rage wutar da ake samu da kashi 30% zuwa 50% a wasu yankuna.

Baya ga haka, lamarin ya sa ana katse wuta na kwanaki da dama musamman a babban birnin kasar, Niamey.

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa Nijar ta dawo aiki da sola gadan gadan tun bayan rage adadin wutar da ake ba su.

Matsalar wutar lantarki a Najeriya

Duk da rage wutar da take tura wa Nijar, Najeriya da kanta tana fuskantar karancin wutar lantarki sakamakon matsalar iskar gas da kuma rashin jari a bangaren samar da wuta.

Kara karanta wannan

Alaƙa ta fara gyaruwa, Tinubu zai tura tagawa Nijar domin isar da saƙonsa ga Tchiani

A halin yanzu, Najeriya na samar da wuta kasa da megawatt 5,000 ga al'umma fiye da miliyan 200.

Masana sun bayyana cewa kasar na bukatar a kalla megawatt 30,000 domin biyan bukatun lantarki yadda ya kamata.

Najeriya na dogaro da iskar gas da ruwa wajen samar da wuta, inda fiye da tashoshin wuta 29 ke amfani da gas.

Najeriya
Najeriya na fama da bashin kudin wutar lantarki. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Amma kalubalen bashin da ke ci gaba da hauhawa ya jefa bangaren cikin wani hali na rashin tabbas.

Bashin wutar lantarki da ake bin Najeriya

Kamfanonin samar da wuta (GenCos) sun yi barazanar dakatar da aiki saboda dimbin bashin suke bin gwamnati da kuma rashin isasshen kudin shiga.

Kungiyar kamfanonin ta bayyana cewa tana bin gwamnati bashin fiye da Naira tiriliyan 4, wanda ya hada da bashin 2024 da kuma tsofaffin basussuka da suka kai Naira tiriliyan 1.9.

A yanzu haka dai ba a san ko dakatar da yawan wutar da ake ba Nijar zai kara inganta harkokin wuta a Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Karfin shugaban rikon Rivers zai ragu, majalisa ta kafa kwamitin lura da ayyukansa

Za a hana shigo da kayan sola Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar daina shigo da kayan sola fadin kasar.

Gwamnatin ta ce za a dauki matakin ne domin rage dogaro da kasahen waje da habaka tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai masana harkokin wuta da tattalin arziki sun gargadi gwamnatin da ta sake tunani saboda za a iya shiga wata matsala saboda matakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng