'Hare Haren Ƴan Bindiga': Matasa Sun Fusata, Sun Cinna wa Gidajen Fulani Wuta a Kwara
- Mazauna Kaiama a jihar Kwara sun shiga cikin fargaba bayan matasa sun kai farmaki Fulani bisa zargin suna taimaka wa 'yan bindiga
- Rahotanni sun ce matasan sun kona rugagen Fulani a Kemenji karkashin jagorancin Ibrahim Bature, kafin jami’an tsaro su kai dauki
- A dajin jihar Ekiti kuwa, ‘yan sanda sun cafke mutane tara da ake zargi da garkuwa da mutane, inda rundunar ta bayyana sunayensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Mazauna karamar hukumar Kaiama da ke jihar Kwara sun shiga firgici yayin da matasa suka fara farmakar wasu garuruwan Fulani a yankin.
An rahoto cewa, fusatattun matasa a ranar Alhamis suka farmaki garuruwan Fulani da ke kauyen Kemenji, bisa zarginsu da taimaka wa 'yan bindiga.

Asali: Twitter
Matasa sun gona gidajen Fulani a Kwara
Mai shari kan lamuran tsaro a Arewa maso Gabas da Tafkin Chadi, Zagazola Maka ya wallafa rahoton a shafinsa na X, a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton Makama ya nuna cewa matasan sun zargi makiyayan da ke zaune a garuruwan da ba 'yan bindiga mafaka ta taimaka masu a garkuwa da mutane da kisan kai.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa matasan bisa jagorancin wani Ibrahim Bature, sun dura rugagen Fulani, inda suka cinna wa rugar wuta kafin barin wajen.
Bayan samun wannan rahoton, dakarun rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro suka kai daukin gaggawa inda abin ya faru.
Jami'an tsaro sun aika sako ga mazauna Kwara
An ce jami'an tsaron sun yi nasarar dawo da zaman lafiya, yayin da ake kokarin kama jagoran matasan da 'yan tawagarsa wadanda a yanzu suka tsere.
Jami'an tsaron sun kuma ba da tabbacin cewa an dawo da doka da oda tare da gargadin jama'ar garin da su guji daukar doka a hannu.
An shawarci mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankulansu yayin da jami'an tsaro suka dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.
'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane

Asali: Twitter
A wani labarin kuma, an ce 'yan sanda sun samu nasarar cafke wasu mutane tara da ake zarginsu da ayyukan garkuwa da mutane a dajin Ekiti.
'Yan sandan sashen kai daukin gaggawa (RRS) suka cafke mutane a dajin Ise/Emure da ke makotaka da Emure-Ekiti a jihar Ekiti da Emure-Ile a jihar Ondo.
Majiyoyi sun shaidawa manema labarai cewa an kai samame kan wadanda ake zargin da misalin 6:35 na yammacin Alhamis, 17 ga Afrilu.
Wadanda ake zargin sun hada da Sanusi Alhaji, Suleiman Ibrahim, Muritala Amodu, Seidu Muhammed, Tairu Amodu, Jibi Alhaji, Saleh Yau, Ibrahim Usman da Mohammed Yau.
A halin yanzu suna hannun hukuma ana ci gaba da yi musu tambayoyi, yayin da bincike ke gudana don gano rawar da suka taka a sace-sacen mutane da aka dinga yi a yankin.
An kai wa Fulani makiyaya hari a Filato
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar Miyetti Allah ta yi Allah-wadai da kisan wasu Fulani makiyaya da aka yi yayin da suke kiwon dabbobinsu a Filato..
Shugaban kungiyar, Babayo Yusuf, ya bayyana sunayen wadanda aka kashe, yana mai cewa har da shanu da dama aka bindige a harin da aka masu.
Ya ce sun riga sun sanar da hukumomin tsaro domin tabbatar da an bi wa makiyayan da aka kashe hakkinsu, duba da cewa ba su aikata laifi ba.
Asali: Legit.ng