Yanzu Yanzu: Matasan Plateau sun kai hari Rugar Fulani, sun kona gidaje 23 da masallaci
- Fusatattun matasa sun kai hari Rugar makiyaya a karamar hukumar Bokkos biyo bayan kisan wasu mutane 13 a kauyen Kwatas da ke yankin
- Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da rakwarata ta GAN Allah, sun tabbatar da harin, inda suka bayyana lamarin a matsayin abun Allah wadai da rashin Imani
- Kungiyoyin sun bayyana yadda aka rataya lamarin a wuyan makiyaya a yankin a matsayin abun kaico
A wani lamari mai kama da ramuwar gayya biyo bayan kisan wasu mutane 13 a kauyen Kwatas da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Plateau, wasu fusatattun matasa sun kai hari Rugar makiyaya, inda suka cinna wa gidaje 23 da wani masallaci wuta a yankin.
Da suke jawabi ya manema labarai a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da rakwarata ta GAN Allah, sun tabbatar da harin, inda suka bayyana lamarin a matsayin abun Allah wadai da rashin Imani.
Yayinda suke Allah wadai da harin baya da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13, kungiyoyin sun bayyana yadda aka rataya lamarin a wuyan makiyaya a yankin a matsayin abun kaico.
A cewarsu, bai kamata a yanke hukuncin cewa makiyaya ne suka yi harin ba domin babu hujjar da ke tabbatar da hakan.
Yayinda ya ke kira ga gwamnati da hukumomin tsaro a kan su yi bincike da tsamo masu laifin ko su fuskanci doka, Mista Bappa ya bukaci dukkanin mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu sannan su rungumi zaman lafiya.
KU KARANTA KUMA: NEPA 2: Yadda wani matashi ya yi mutuwar ban tausayi a jahar Jigawa
A halin da ake ciki, Gwamnan jihar Plateau kuma Shugaban gwamnonin Arewa, Simon Lalong a ranar Talata, 28 ga watan Janairu ya yi umurnin dukkanin shugabannin Fulani a kananan hukumomin Bokkos, Mangu, Riyom da Barkin Ladi da ke jihar yayinda yawan mutanen da suka mutu a harin karshen mako ya tasar na 22.
Lalong ya bayar da umurnin ne ga kwamishinan yan sanda, Isaac Akinmoyede a lokacin wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki, shugabannin Fulani da shugabannin garuruwa da na addini wanda ya gudana a gidan gwamnati a Jos.
Gwamnan wanda ya fusata da nuna bakin ciki a kan cigaba da kai hare-haren da kashe-kashe da yan bindiga ke kaiwa wasu kauyuka a Bokkos da Mangu, ya ce ba zai sake lamuntan haka ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng