Akwai hannun manyan 'yan siyasa a yawan sace-sacen mutane, gwamna Ortom

Akwai hannun manyan 'yan siyasa a yawan sace-sacen mutane, gwamna Ortom

- Gwamnan jihar Benue ya bayyana cewa, akwai hannun 'yan siyasa a rashin tsaron kasar nan

- Ya kuma bayyana yadda 'yan siyasa suka shigo da sojojin kasashen waje don aikata barna a kasar

- Ya kuma ce, watsi da sojojin hayan ne ya jawo tabarbarewar tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa wasu jami’an gwamnatin Najeriya na hada baki da masu satar mutane don aikata mummunan aikinsu, Arise Tv ta ruwaito.

Mista Ortom ya ce 'yan siyasar da ke da wata manufa sun shigo da sojojin haya na kasashen waje don taimaka musu su ci zaben 2019. Ya lura cewa watsi da wadannan sojojin haya shi ya haifar da tabarbarewar yanayin tsaro a kasar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da yake gabatar da lacca a Makon 'Yan Jaridu na 2021 mai taken: "Rashin tsaro a Najeriya: Maido da Zaman Lafiya, Hadin kai da Ci gaba" kuma kungiyar Hadin kan 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Hukumar NAFDAC ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnati

Akwai hannun manyan 'yan siyasa a yawan sace-sacen mutane, gwamna Ortom
Akwai hannun manyan 'yan siyasa a yawan sace-sacen mutane, gwamna Ortom Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

"Akwai wani kasuwancin da ke kawo riba a Najeriya tare da tsananin zaton hada kai da jami'an Gwamnati," in ji gwamnan.

“Karuwar sace-sacen mutane a kowane bangare a fadin kasar lamari ne mai hatsari. Ba mu san wanda yake fadin gaskiya ba.

"Amma kamar yadda yake a yanzu, akwai zargi mai karfi da ke nuna cewa 'yan siyasar da ke cikin wahala sun shigo da sojojin haya na kasashen waje don taimaka musu su ci zabe.

"Abin takaici, bayan da aka fadi zabe aka kuma ci nasara, aka yi watsi da sojojin hayan wadanda ke haifar da tabarbarewar tsaro a kasar."

KU KARANTA: Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

A wani labarin, Baya ga makudan kudaden da ake biya a matsayin fansa ga masu satar mutane daga iyalan mutanen da aka sace, a yanzu haka ‘yan bindigan sun nemi a basu buhunan shinkafa da kayan miya a matsayin wani bangare na fansa.

Al’umomin karkara da ke yankunan Kuje, Kwali, Gwagwalada da kuma Abaji sun shaida ci gaba da kai hare-hare, inda aka sace sama da mutane 30 a cikin watanni uku da suka gabata kuma suka karbi kudin fansa na miliyoyin nairori.

Amma kwanan nan, yayin sace wasu mazauna yankin Kiyi da Anguwar Hausawa, masu garkuwar sun gaya wa iyalan wadanda suka yi garkuwar da su kawo buhunan shinkafa, taliya, supageti da kuma katan din maggi tare da kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel