Yan Sanda Sun Yi Bajinta, Sun Kau da Kai daga Cin Hancin N1m
- Rundunar ‘yan sandan Katsina ta cafke Mubarak Kabir da Adamu Hashim, wadanda ake zargi da satar mota daga Abuja
- Masu laifin sun nemi ba wa jami’an tsaro cin hanci na Naira miliyan daya domin su kubuta, amma 'yan sandan su ka ki karɓa
- Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina, CP Bello Shehu, ya yaba da kishin kasa da gaskiyar jami’an da suka ki karbar kudin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Rundunar ‘yan sandan Katsina ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar mota.
An damke su ne a lokacin da suka yi yunkurin ba wa jami’an tsaro cin hanci na Naira miliyan daya domin su kubuta daga hannunsu.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, lamarin ya faru ne a ranar 11 ga Afrilu, 2025, misalin karfe 3:00 na rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DSP Aliyu ya bayyana cewa jami’an da ke aiki a sashen kula da iyakokin kasa na shiyya ta 4 da ke Katsina, sun dakatar da wata mota kirar Toyota Corolla LE.
‘Yan sanda sun ki karbar cin hancin N1m
A cewar The Punch, mutanen da ke cikin motar su ne Mubarak Kabir, mai shekaru 26, da kuma Adamu Hashim, mai shekaru 27, dukkansu mazauna Kurna a karamar hukumar Fagge da ke Kano.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa motar an sace ta ne daga babban birnin tarayya, Abuja, kuma a lokacin da matasan suka fuskanci an kama su, sai suka nemi ba da cin hanci.

Asali: UGC
Ana zargin sun miƙa musu cin hanci na Naira miliyan daya, sai dai jami’an sun yi biris da tayin kudin, inda suka kama su tare da kai su caji ofis.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da motar da aka sace, kudi Naira miliyan daya, waya guda uku, “power bank” guda daya, da kuma makullai da dama.
Jami'an ‘Yan sanda na binciken satar mota
Yanzu haka, jami'an yan sandan na ci gaba domin gano cikakken rawar da wadanda ake zargin suka taka a cikin harkar laifi.
DSP Sadiq ya tabbatar wa al’umma cewa za su ci gaba da bayar da bayani kan cigaban da ake samu yayin da binciken ke gudana.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina, CP Bello Shehu, ya yaba wa jami’an da suka ki karbar cin hancin bisa kishin kasa, jajircewa da amana.
Ya kuma jaddada kudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da bin ka’ida da kare hakkin dan Adam.
'Yan sandan Kano sun yi kamu
A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu nasarar bankaɗo wata ƙungiya da ke safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba a jihar Kano, lamarin da ya kai ga cafke mutane uku.
A cewar sanarwar da rundunar ta fita, an kama wadanda ake zargi da safarar makaman ne a ranar 10 ga Afrilu, 2025, a unguwar Dorayi Babba da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kwato bindigu 15 da aka ƙera a gida da harsasai 102 a hannun wadanda ake zargin, yayin wani samame da suka kai yankin.
Asali: Legit.ng