Muhyi Ya Kare Kansa bayan Zargin Tozarta Ma'aikatan Gwamnatin Kano saboda Ƴar Tikok
- Shugaban hukumar yaki da rashawa na Kano, Muhyi Magaji Rimingado ya musanta cewa yana da alaka da fitacciyyar 'yar tiktok, Rahama Sa'idu
- ‘Yan Kwankwasiyya sun caccaki Muhyi bisa rushewar allon tallan Rahama Sa’idu, inda suka zarge shi da cin mutuncin jami’an gwamnatin Kano
- Muhyi ya ce dokar PCACC ta ba shi damar karɓar kowanne ƙorafi daga ɗan jihar, kuma sashi na tara na dokar ya umarci sauraren irin waɗannan koke
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano (PCACC), Muhyi Magaji Rimin Gado, ya kare kansa bayan zargin cewa ya zakalkale a kan wata 'yar TikTok, Rahama Sa’idu.
Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta, musamman 'yan Kwankwasiyya, sun zargi Muhyi da cin mutuncin manyan jami’an gwamnatin Kano saboda rushe allon tallan shagon Rahama.

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da DCL Hausa, Muhyi ya bayyana cewa ya kira jami’an hukumar raya birane ta Kano (KNUPDA), saboda ƙorafin da matashiyar ta yi cewa ba a yi mata adalci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bidiyon da ya tayar da kura, an hango Muhyi yana tada jijiyar wuya kan rushe allon Rahama a titin UDB, ya bayar da umarnin a gaggauta mayar mata da allonta, domin an karya doka.
Kano: Muhyi ya nesanta kansa da Rahama
A wata hira da NNPP Kwankwasiyya ta wallafa a shafinta na Facebook, shugaban hukumar PCACC ya ce ya karɓi ƙorafin Rahama Sa’idu ne a matsayinta na mazauniyar Kano mai ƙorafi.
Ya ce:
"Alaƙa ɗaya ce kawai, ita ce dokar ta tanadi cewa duk wanda ya kawo ƙorafi za mu saurare shi. Allah ne shaida."
"In kuma wasu ne a hukumar yaƙi da rashawa, ban sani ba. Amma tun da ni ne shugaban kowa a wurin, ya kamata a ce ni ne ake zargi da wannan."
"Kuma ni ban san waɗanda suka zo wurin ba, ba ita kaɗai ba — duk wanda suka kawo ƙorafin nan, ba wanda na sani tun asali."
Dalilin Muhyi na karɓar ƙorafin Rahama
Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana cewa dokar da ta kafa hukumar PCACC ta ba shi damar karɓar ƙorafin duk wani ɗan Kano ko mazaunin jihar da ke ganin an yi masa ba daidai ba.
Ya bayyana cewa ba ‘yar TikTok din ce kaɗai ba ce ta kawo ƙorafi ba, akwai wasu mutane da suka zo tare da ita, kuma an duba lamarinsu baki ɗaya na rushe allunansu a UDB.

Asali: Facebook
Muhyi ya ce:
"Hukumar (PCACC) tana da ikon gudanarwa, ko dai a karan-kanta, ko idan an kawo mata ƙorafi, ta duba dukkannin dokokin gudanarwa na gwamnati ko na ma'aikata, ko wani ma’aikaci."
Ya ƙara da cewa duk wanda ke ganin ya aikata ba daidai ba, zai iya nuna sashen dokar da hukumar PCACC ta karya a wannan batu.
Muhyi ya ce sashe na tara ne ya ba su umarnin sauraren ƙorafin duk mai ƙorafi da yake ganin an taka masa hakki a cikin jihar Kano.
Hisbah ta kama matashi a Kano
A wani labarin, kun ji cewa hukumar Hisbah a jihar Kano ta cafke wani matashi bisa zargin aikata baɗala da dabba, lamarin da ya janyo surutu kafafen sada zumunta na zamani.
An kama matashin mai suna Shamsu Yakubu, mai shekaru 24 da haihuwa, wanda ya fito daga karamar hukumar Dawakin Tofa, bayan wani bidiyo da ya yadu a TikTok a kwanan nan.
A jawabinsa, Mataimakin Kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Mujahidden Aminuddeen Abubakar, ya bayyana cewa abin da matashin ya aikata babban laifi ne a Musulunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng