'Tinubu na da Sauran Aiki': An Ji Lokacin da Tattalin Arzikin Najeriya Zai Gyaru

'Tinubu na da Sauran Aiki': An Ji Lokacin da Tattalin Arzikin Najeriya Zai Gyaru

  • Bankin Duniya ya tabbatar da goyon bayansa ga gyaran tattalin arzikin Tinubu da shirin Renewed Hope yayin ziyarar tawagarsa a Abuja
  • Ousmane Diagana ya jinjinawa ci gaban GDP da ya kai 3.4% tare da bukatar ci gaba da sauye-sauyen da ke kawo cigaba da aiki ga jama’a
  • Wale Edun ya bayyana niyyar gwamnati na kammala ayyuka da hanzarta Mission 300 da kara tallafi kai tsaye ga mutane miliyan 15

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Bankin Duniya ya sake jaddada goyon bayansa ga tsarin gyaran tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu da manufofin Renewed Hope na gwamnatin Tarayya.

Bankin ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da shugabanninsa suka kai wa ministan Kudi, Wale Edun a babban birnin tarayya Abuja.

Bankin Duniya ya yi magana kan tasirin manufofin gwamnatin Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu (Hagu), Ginin Bankin Duniya (Dama). Hoto: Bola Ahmed Tinubu, World Bank
Asali: Facebook

Mohammed Manga, daraktan watsa labarai na ma'aikatar kudi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin Duniya ya jinjinawa gwamnatin Tinubu

Tawagar Bankin Duniya, wadda mataimakin shugaban bankin na Yammaci da Tsakiyar Afirka, Ousmane Diagana, ya jagoranta, ta ce tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 3.4%, mafi girma tun 2014.

Ousmane Diagana ya jinjinawa matakan da gwamnati ke dauka wajen daidaita tattalin arziki da inganta ayyukan da ke karkashin Bankin Duniya a kasar.

Sanarwar Manga ta kara da cewa:

"Diagana ya jaddada bukatar ci gaba da aiwatar da sauye-sauye domin cimma bunkasar tattalin arziki da zai fitar da jama'a daga talauci da samar da ayyukan yi.
"Haka kuma ya bayyana cewa Najeriya ce kasa mafi girman alaka da Bankin Duniya a Afirka, inda ta kulla alakar kudaden da suka kai har dala biliyan 17."

An ji lokacin da tattalin arziki zai daidaita

Bugu da kari, Diagana ya yaba da jagorancin Najeriya a shirin Mission 300, wani kokari na nahiyar Afirka domin samar da wutar lantarki ga mutane miliyan 300.

Shugaban ya kuma bukaci a gaggauta aiwatar da shirye-shiryen tallafin gwamnati, musamman tsarin rabon kudi kai-tsaye ga mabukata.

Sanarwar Manga ta kara da cewa:

"Tare da goyon bayan Bankin Duniya da kudurinsa na taimakawa Najeriya a fannin sauye-sauyen tattalin arziki, ana sa ran kasar za ta cimma manyan nasarori a nan gaba."

Bankin Duniya ya nuna cewa Najeriya na bukatar ci gaba da wadannan sauye-sauye na tsawon shekara 10 zuwa 15 domin sauya fasalin tattalin arzikinta.

Minista ya fadi tsare-tsaren gwamnatin Tinubu

Ministan kudi, Wale Edun ya karbi bakuncin shugabannin Bankin Duniya.
Ministan kudi, Wale Edun. Hoto: Diershman
Asali: Facebook

A nasa bangaren, ministan kudi Wale Edun ya sake tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na da kudurin ci gaba da aiwatar da manufofin Tinubu domin saukaka rayuwar ‘yan Najeriya.

Edun ya ce gwamnati za ta maida hankali ne a kan abubuwa uku: saurin kammala ayyuka, kara yawan wadanda ake ba tallafi gwamnati zuwa mutane miliyan 15 da hanzarta aiwatar da shirin Mission 300.

A bangaren hadin gwiwa, an jaddada mahimmancin kara yawan amfanin gona, samar da hanyoyin samun jari ga kananan da matsakaitan masana’antu (SMEs), inganta fasahar zamani da fayyace tsarin hada-hadar kudi ga kowa da kowa.

Tinubu zai kinkimo bashin $300m

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman bashin dala miliyan 300 daga Bankin Duniya domin inganta harkar lafiya a Najeriya.

Za a aiwatar da shirin ne karkashin kulawar hukumar NCDC, yayin da ma’aikatar kudi za ta jagoranci karɓar bashin a madadin gwamnati.

Bankin Duniya zai duba da tantance shirin a watan Afrilu 2025, sannan a yanke hukuncin bayar da bashin a Yuli, don fara aiki a shekarar 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.