'Yan Sanda Sun Yi Kazamin Musayar Wuta da 'Yan Bindiga, an Samu Asarar Rayuka
- Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya masu aikin samar da tsaro sun yi gumurzu da ƴan bindiga a jihohin Abia da Nasarawa
- Ƴan sandan sun samu nasara hallaka ƴan bindiga guda bakwai tare da ƙwato makamai masu tarin yawa
- Jami'an tsaron sun kuma yi nasarar kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su bayan sun yi gumurzu da miyagun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jami’an hukumar ƴan sanda a jihohin Abia da Nasarawa, sun ragargaji ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.
Jami'an ƴan sandan sun hallaka masu garkuwa da mutane guda bakwai a yayin musayar wuta, sannan sun ceto mutane huɗu da aka sace.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sanda na ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Lahadi, a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun kashe ƴan bindiga
A yayin samamen, ƴan sandan sun ƙwato bindigogi biyu ƙirar AK-47, jigida guda shida, da harsasai guda 34.
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa an kai mutanen da aka ceto zuwa asibitin ƴanda domin samun kulawa.
“A ƙoƙarin daƙile garkuwa da mutane, wanda wasu bata-gari ke ɗauka a matsayin hanyar samun kuɗi, da kuma hana aikata miyagun laifuka da suka shafi amfani da bindiga, jami’an hukumar ƴan sandan Najeriya sun sake samun gagarumar nasara."
“Don daƙile waɗannan munanan laifuka, musamman garkuwa da mutane da safarar makamai, jami’an ƴan sanda a Abia da Nasarawa sun aiwatar da samame na musamman wanda ya kai ga kubutar da mutanen da aka sace, kashe wasu daga cikin ƴan ta’adda, da kuma ƙwato makamai da harsasai.”
“A ranar 9 ga Maris, 2025, da misalin ƙarfe 9:30 na safe, rundunar ƴan sandan jihar Abia ta samu rahoton cewa wasu mutane huɗu sun shiga hannun ƴan bindiga yayin da suke tafiya a cikin motarsu ƙirar Toyota RAV4 a kan titin New Umuahia, Obingwa."
"Bisa ga sahihan bayanan sirri da aka samu, tawagar jami’an tsaro ta gano maɓoyar masu garkuwa da mutanen a ranar 14 ga Maris, 2025, a wani gida mai ɗakuna uku da ke Osokwa, ƙaramar hukumar Osisioma."
"Da jami’an tsaro suka isa wurin, ƴan bindigan sun buɗe musu wuta. Sai dai, jami’an sun yi nasarar fatattakar su, inda suka hallaka mutane guda shida, sannan suka ceto mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya."
"A gefe guda kuma, rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, tare da haɗin gwiwar Sojojin Najeriya da ƴan sa-kai, sun samu nasarar kashe wani sanannen mai garkuwa da mutane mai suna Abdullahi, wanda aka fi sani da ‘Honor’, yayin wani sumame da aka kai a Akwanga a ranar 14 ga Maris, 2025.”
“Wannan mutumin da aka kashe yana cikin jerin waɗanda hukumomi ke nema ruwa a jallo saboda aikata laifuka da dama. An kama shi kusa da Masallacin Juma’a na Akwanga yayin da yake ƙoƙarin tserewa da babur.”
- ACP Olumuyiwa Adejobi
Muyiwa Adejobi ya bayyana cewa Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya jinjinawa jami’an tsaron bisa ga ƙwazon da suka nuna.
Jami'in ɗan sanda ya kashe wani mutum
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jam'in rundunar ƴan sandan Najeriya ya hallaka wani mutum har lahira a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.
Lamarin wanda ya auku a garin Maitumbi ya faru ne bayan ɗan sandan ya buɗe wuta kan wasu mutane sakamakon giyar da ya kwankwaɗa.
Asali: Legit.ng