Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyuka cikin Dare, Sun Sace Bayin Allah

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyuka cikin Dare, Sun Sace Bayin Allah

  • Wasu tantiran ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun kai hare-haren ta'addanci a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna
  • Tsagerun ƴan bindigan sun farmaki wasu ƙauyuka guda uku na ƙaramar hukumar a cikin daren ranar Laraba
  • Mutanen yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakan ganin sun kare rayuka da dukiyar al'umma

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hare-hare a ƙauyuka uku na ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun sace mutum 10 daga ƙauyukan a hare-haren da suka kai cikin dare.

'Yan bindiga sun kai hare-hare a Kaduna
'Yan bindiga sun sace mutum 10 a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru da a daren ranar Laraba, da misalin ƙarfe 2:00.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka farmaki ƙauyuka

Gungun ƴan bindigan ɗauke da makamai sun afkawa ƙauyen Unguwan Yashi-Maraban Kajuru tare da yin garkuwa da mutum shida.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun yi rashin imani, sun tashi mutanen garuruwa 5 ana azumi

Mutanen da aka sace sun haɗa da God-Dream Ladan, Lady God-Dream, Philip Mudakas, Mercy Philip, Bitrus Philip, da Gmen Philip.

Haka nan a ƙauyen Makyali, ƴan bindiga sun jikkata mutane biyu sakamakon harbin bindiga, inda a halin yanzu suke karɓar magani a Asibitin Maraban Kajuru.

Haka kuma, an sace wasu mata biyu, Rahina Yahaya da Zulai Yahaya a wannan ƙauyen.

An bayyana sunayen waɗanda suka jikkata sakamakon harbin bindigan da Ubale Yahaya da Abdullahi.

Bayan haka, an samu labarin cewa ƴan bindigan sun sake kai hari a Ungwan Mudi Doka da misalin ƙarfe 4:00 na dare, inda suka yi garkuwa da wasu mutum biyu, Amos Michael da Samita Amos.

Muƙaddashin Hakimin Kufana, Stephen Maikori, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa sun samu sauƙi hare-haren ƴan bindiga a kwanakin baya, amma a cikin wannan makon sun sake dawowa.

"Ya zuwa yanzu, an sace mutum 10, yayin da wasu mutum biyu ke jinya. Muna roƙon hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen kawo ɗauki da daukar matakin gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a wannan yanki."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace matashin da ya lashe gasar Kur'ani bayan ya gana da gwamna

- Stephen Maikori

Ya kuma bayyana cewa an sanar da hukumomin tsaro dangane da harin da ƴan bindigan suka kai.

Me hukumomi suka ce kan harin?

A halin yanzu, gwamnatin jihar Kaduna da rundunar ƴan sanda ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Hazalika ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun sace mahaddacin Al-Kur'ani

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun sace wani matashi da ya lashe gasar karatun Al-Kur'ani a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

Ƴan bindigan sun sace matashin ne tare da ƴan uwansa bayan ya gana da Gwamna Dikko Umaru Radda wanda ya karrama shi.

Miyagun ƴan bindigan sun sace shi ne a ƙauyen Labin Bangori cikin ƙaramar hukumar Faskari ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng