Sojoji Sun Gwabza Fada da 'Yan Bindiga, Sun Hallaka Miyagu a Zamfara
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile harin wani ƴan bindiga a jihar Zamfara da ke kuka da 'yan bindiga
- Sojojin sun samu nasarar ne bayan ƴan bindiga sun kawo farmaki a garin Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau
- Bayan an gwabza faɗa, dakarun sojojin sun yi nasarar fatattakar ƴan bindigan inda suka yi nasarar hallaka wasu daga cikinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma tare da hadin gwiwar ƴan sa-kai, sun daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun daƙile harin ne a garin Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau, jihar Zamfara, inda suka kashe ƴan bindiga huɗu.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun daƙile harin ƴan bindiga
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare a ranar Juma’a, kuma yana cikin jerin hare-haren ramuwar gayya da ƴan bindiga ke kai wa a garin tun bayan kashe wani shahararren jagoransu da ke addabar al’ummar yankin.
Wata majiya daga ɓangaren tsaro ta bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, dakarun soji da ƴan sa-kai sun yi gaggawar fuskantar ƴan bindigan.
Jami'an tsaron sun yi musayar wuta mai tsanani da tsagerun wacce ta tilasta musu tserewa cikin daji da raunukan harbin bindiga.
"Ƴan bindiga sun kutsa cikin garin da nufin haddasa tashin hankali, amma jami’an tsaro da ƴan sa-kai sun mayar da martani cikin gaggawa. Mun kashe huɗu daga cikinsu, yayin da sauran suka gudu ɗauke da raunuka."
- Wata majiya
Wani mazaunin garin, mai suna Naziru Bakanike Mada, ya samu raunin harbin bindiga a kafadarsa yayin musayar wutar, kuma an garzaya da shi zuwa asibiti don kula da lafiyarsa.
Ƴan bindiga na kai hare-hare a Mada
Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan hari na ranar Juma’a shi ne karo na huɗu da ƴan bindiga suka yi kokarin kutsawa garin Mada.
Ƴan bindigan na son yin ramuwar gayya ne tun bayan da sojoji suka kashe jagoransu, Alhaji Sani Dan Garin Bawo, a wani gagarumin farmakin da suka kai a baya.
Tun daga ranar 11 ga watan Maris, ƴan bindiga da ke biyayya ga Dogo Hamza, wanda aka kashe, sun sha kai hare-hare a kan garin Mada.
Sai dai, duk da haka, jami’an tsaro sun ci gaba da daƙile duk wani yunƙurin su, tare da hallaka da dama daga cikinsu.
Wani jami’in soja ya bayyana cewa cewa:
"Mada ya zama maƙabarta ga ƴan bindiga. Su ci gaba da zuwa domin jaraba sa'arsu, mu kuma za mu ci gaba da aika su wurin Mahaliccinsu."
Sojojin sama sun ragargaji ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma sun yi ruwan wuta kan ƴan bindiga a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun hallaka ƴan bindiga masu yawa a farmakin da suka kai musu a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng