Tinubu Ya Fadi Aikin da Ya yi da Aka Gaza Lokacin Buhari, Jonathan, 'Yar'adua

Tinubu Ya Fadi Aikin da Ya yi da Aka Gaza Lokacin Buhari, Jonathan, 'Yar'adua

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce tsawon shekaru 50 Najeriya na kashe kudin wadanda ba a haifa ba wajen yin tsare tsare marasa karko
  • Rahotanni sun nuna cewa Tinubu ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka sun hana tattalin arzikin ƙasa durƙushewa a yau
  • Tsofaffin sanatoci daga Jamhuriyya ta Uku sun yaba da shirye-shiryen tallafin karatu da na basussuka da ake ba ‘yan ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta dade tana cin kudin 'yan kasa da za a haifa a gaba, wanda hakan ya haddasa matsalolin tattalin arziki.

Ya bayyana hakan ne a fadar gwamnati da ke Abuja, yayin da ya karɓi bakuncin tsofaffin ‘yan majalisar dokoki na Jamhuriyya ta Uku.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya hada Buhari da Tinubu, ya yi musu rubdugu a sabon littafinsa

Tinubu
Bola Tinubu ya ce an fara ganin haske a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa Tinubu ya ce a bisa dole aka ɗauki matakan don hana ƙasar durƙushewa gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya kuma gode wa ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suka bayar a kan matakan tattali da ya dauka.

Tinubu: Najeriya ta fuskanci barazanar tattali

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa da ba a ɗauki matakan da aka ɗauka ba, da tattalin arzikin ƙasar ya durƙushe.

Shugaban kasar ya ce:

“Mun fuskanci manyan matsaloli a lokacin da muka karɓi mulki. Idan ba mu ɗauki matakin da muka ɗauka ba, da yanzu bashi ya yi wa Najeriya katutu.”

Haka zalika, ya jaddada cewa gwamnatinsa ta samu nasarar daidaita matsalar kuɗi, inda darajar Naira ke fara daidaita:

“Yanzu an fara ganin haske. Farashin kayayyaki na raguwa, musamman a lokacin Ramadan.”

Kara karanta wannan

Al-Mustapha ya ziyarci Atiku awanni da sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP

Tinubu: Dimokuradiyya ce mafita ga Najeriya

Shugaban ƙasar ya ce jajircewa a kan tafarkin dimokuradiyya ce hanya mafi dacewa da za ta kawo ci gaba a ƙasar.

Haka nan, Tinubu ya ce yana farin ciki da yadda tsofaffin Sanatocin suka ci gaba da ba da goyon baya ga dimokuradiyya da ci gaban ƙasa.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Tsofaffin Sanatoci sun yaba wa Bola Tinubu

Sanata Emmanuel Chiedoziem Nwaka, wanda ya yi magana a madadin tawagar, ya yaba da shirye-shiryen tallafin karatu da na basussuka ga ‘yan ƙasa.

Tsohon Sanatan ya ce:

“Ina yaba maka bisa taimakon da kake bai wa ɗalibai. Na tattauna da su, kuma da dama sun ci moriyar shirin.”

Haka kuma, ya bayyana shirin basussuka na CREDICORP a matsayin wata hanya da za ta rage cin hanci da rashawa.

Emmanuel Chiedoziem Nwaka ya ce:

“Yanzu matasa na iya samun rancen sayen mota ko gida ba tare da sun tara dukiyar da ba su da ita ba.”

Kara karanta wannan

Matawalle: Ministan tsaro ya canja salon raba tallafin azumi, ya ba da N500m

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Sanata Bako Aufara Musa, Hon. Terwase Orbunde, Hon. Wasiu Logun, Hon. Amina Aliyu, Cif Obi Anoliefo da Hon. Eze Nwauwa.

An ware talakawa miliyan 68 don tallafa musu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa an ware sunayen talakawa miliyan 68 domin tallafa musu.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnati ta zakulo sunayen mutanen ne daga dukkan jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng