Tinubu Ya Juyawa Majalisar Tarayya baya kan Kirkirar Sababbin Jami'o'i 200 a Najeriya

Tinubu Ya Juyawa Majalisar Tarayya baya kan Kirkirar Sababbin Jami'o'i 200 a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan akalla kudirori 200 da majalisar tarayya ke kokarin gabatarwa don kafa sababbin jami’o’i a kasar
  • Ministan ilimi, Tunji Alausa, ya ce Najeriya na da jami’o’i 278, amma yawancinsu ba su da wadatattun kayan aiki ko isassun damar daukar dalibai
  • Ya ce maimakon kafa sababbin jami’o’i, ya fi dacewa a bunkasa wadanda ake da su, a gina dakunan gwaje-gwaje da daukar kwararrun malamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta nuna adawa da kudirin majalisar tarayya na kafa sababbin jami’o’i kusan 200 a fadin Najeriya.

Ministan ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana hakan a Abuja yayin taron manema labarai na shekarar 2025 da ma’aikatarsa ta shirya.

Gwamnatin tarayya ta magantu kan daruruwan jami'o'i da majalisa ke so a kafa
Gwamnatin tarayya ta kalubalanci kudurorin majalisa na kirkirar sababbin jami'o'i 200. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Gwamnati ta dakatar da kafa sababbin jami'o'i

A cewar Tunji Alausa, akwai damuwa kan yadda ake yawan kirkirar jami’o’i, alhalin cewa babu isassun kayan aiki a tsarin ilimi na kasar, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoto ya nuna cewa Najeriya na da jami’o’i 278, inda 64 ke karkashin gwamnatin tarayya, 67 mallakin jihohi, sannan 147 na masu zaman kansu ne.

A watan da ya gabata, gwamnati ta sanar da dakatar da kafa sababbin jami’o’in kudi na tsawon shekara guda domin tabbatar da inganci da dorewar na yanzu.

Majalisa na so a kafa sababbin jami'o'i 200

Jaridar The Sun ta rahoto ministan ya ce maimakon kafa sababbin jami’o’i, ya fi dacewa a kara inganta wadanda ake da su don su ba da ingantaccen ilimi.

Tunji Alausa ya ce:

“A yanzu muna da kusan kudirori 200 a majalisa na kafa sababbin jami’o’i. Ba za mu iya ci gaba da tafiya a wannan tsarin ba.
“Muna da jami’o’i masu yawa, amma ba su da isassun damar daukar dalibai. Abin da ya kamata mu yi shi ne mu inganta su.

Kara karanta wannan

Matawalle: Ministan tsaro ya canja salon raba tallafin azumi, ya ba da N500m

“Dole mu daina wannan dabi’a ta kafa sababbin jami'o'i. Muna bukatar bunkasa kayan aiki, gina dakunan gwaje-gwaje, da daukar malamai masu inganci.”

Yawan dalibai ya yi kadan a wasu jami'o'i

Ministan ilimi, Tunji Alausa ya yi magana kan kafa sababbin jami'o'i a Najeriya
Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, a wajen taron kaddamar da NEDI. Hoto: @DrTunjiAlausa
Asali: Twitter

Ministan ya bayyana cewa daga cikin daliban da ke karatu a jami’o’i, kashi 7.5% ne kacal ke a jami’o’i na masu zaman kansu.

Tunji Alausa ya kara da cewa:

“Yawan daliban da ke karatu a jami’o’i a Najeriya bai wuce 875,000 ba, adadi ne da bai kai yadda ya kamata a samar da karin daruruwan jami'o'i ba.
“Wasu jami’o’in ma ba su da fiye da dalibai 1,000, amma har yanzu ana matsin lamba na kafa sababbin jami’o’i. Dole mu dakatar da hakan.”

Tinubu ya amince a kafa sababbin jami'o'i 11

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaban kasa Bola Tinubu, ya amince da kafa sababbin jami’o’i 11 masu zaman kansu a Najeriya don habaka ilimi.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu sun hada kai, ana shirin samawa matasa miliyan 5 aiki

Ministan ilimin Najeriya, Tunji Alausa, ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa (FEC) da aka gudanar a ranar Litinin, 3 ga Maris, 2025.

Tunji Alausa ya bayyana cewa an bai wa jami’o’in lasisin wucin gadi, kuma gwamnati za ta sa ido don tabbatar da cika sharuɗɗan hukumar NUC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng