Sunayen Sababbin Jami’o’i 37 Da NUC Ta Ba Lasisi Kafin Buhari Ya Bar Ofis

Sunayen Sababbin Jami’o’i 37 Da NUC Ta Ba Lasisi Kafin Buhari Ya Bar Ofis

  • Daf da Muhammadu Buhari zai sauka daga kan mulki, aka amince a kafa wasu sababbin jami’o’i
  • Hukumar NUC ta kasa, ta bada lasisin fara aiki ga wadannan jami’o’i 37 da ‘yan kasuwa su ka kafa
  • Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya ce yanzu akwai jami’o’in ‘yan kasuwa fiye da 140 a fadin kasar

Abuja - A ranar 15 ga watan Mayu 2023, majalisar zartarwa ta kasa watau FEC, ta amince da karin kafa wasu jami’o’i da za su soma karantarwa a Najeriya.

Vanguard ta ce hukumar NUC ta ba wadannan makarantu lasisi a hedikwatarta da ke babban birnin Abuja.

Shugaban NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya tabbatar da cewa hakan ya jawo jami’o’in da ake da su domin samun digiri a kasar nan sun kai 264.

Sababbin Jami'o'i
Sunayen sababbin Jami'o'i Hoto: www.legit.ng
Asali: UGC

Gwamnatin tarayya ta karkashin NUC, ta yi kira ga wadanda su ka kafa jami’o’in su dage wajen ganin an ci ma manufa, ba kudi kurum aka sa a gaba ba.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Ya Dace Kowa Ya Sani Kan Sababbin Shugabannin Soji, IGP da Kwatsam

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta ce jami’o’in da aka ba sababbin lasisi su ne:

1. Rayhaan University (Jihar Kebbi)

2. Muhammad Kamalu-Deen University (Jihar Kwara)

3. Sam Maris University (Jihar Ondo)

4. Aletheia University (Jihar Ogun)

5. Lux Mundi University (Jihar Abia)

6. Maduka University (Jihar Enugu)

7. Peaceland University (Jihar Enugu)

8. Amadeus University (Jihar Abia)

9. Vision University (Jihar Ogun)

10. Azman University (Jihar Kano)

11. Huda University (Jihar Zamfara)

12. Franco British International University (Jihar Kaduna)

13. Canadian University of Nigeria (FCT, Abuja)

Har ila yau akwai:

14. Miva Open University (FCT, Abuja)

15. Gerar University of Medical Sciences (Jihar Ogun)

16. British Canadian University (Jihar Kuros Riba)

17. Hensard University (Jihar Bayelsa)

18. Phoenix University (Jihar Nasarawa)

19. Wigwe University (Jihar Nasarawa)

20. Hillside University of Science and Technology (Jihar Ekiti)

Akwai jami’o’i irinsu:

21. University of the Niger (Jihar Anambra)

22. Elrazi University of Medical Sciences Niger (Jihar Kano)

23. Venite University (Jihar Ekiti)

Kara karanta wannan

DSS Ta Gano Makuden Kudade A Gidan Emefiele? Gaskiya Ta Bayyana

24. Shanahan University (Jihar Anambra)

25. Duke Medical University (Jihar Kuros Riba)

26. Mercy Medical University (Jihar Osun)

27. Cosmopolitan University (FCT, Abuja)

28. Iconic Open University (Jihar Sokoto)

29. West Midland Open University (Jihar Oyo)

30. Amaj University (FCT, Abuja)

Jami'a
Sunayen sababbin Jami'o'i Hoto: www.legit.ng
Asali: UGC

Ragowar su ne:

31. Prime University (FCT, Abuja)

32. El-Amin University (Jihar Neja)

33. College of Petroleum and Energy Studies (Jihar Kaduna)

34. Jewel University (Jihar Gombe)

35. Nigerian University of Technology and Management (Legas)

36. Al-Muhibbah Open University (FCT, Abuja)

37. Al-Bayan University (Jihar Kogi)

Badakala a CBN

An ji labari kungiyar George Uboh Whistleblowers Network ta fallasa rashin gaskiyar Godwin Emefiele a CBN, hakan ya yi sanadiyyar daure George Uboh.

Dr. George Uboh ya na zargin an tafka badakalar canjin kudin fiye da fam Dala biliyan 3 a shekarar 2019. 'Dan kasuwan ya fito ya ba Bola Tinubu shawara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel