Matawalle: Ministan Tsaro Ya Canja Salon Raba Tallafin Azumin, Ya ba da N500m
- Karamin Ministan tsaron Najeriya, Bello Mattawalle, ya rabawa magoya bayan APC a Zamfara N500m domin sauƙaƙa musu azumi
- Bello Matawalle ya canza salo wajen raba kudi, a maimakon kayan abinci, domin wasu ‘yan siyasa sun riga sun raba hatsi a jihar
- Rahotanni sun nuna fiye da kashi 80% na waɗanda aka yi niyyar ba da tallafin dominsu sun riga sun karɓi kuɗin da aka ware musu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Ministan tsaro, Bello Mattawalle, ya bayar da tallafin Naira miliyan 500 ga magoya bayan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara domin sauƙaƙa musu azumin watan Ramadan.
Mai taimaka wa ministan, Ibrahim Danmaliki Gidan-Goga ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Alhamis.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa Gidan-Goga ya ce maimakon raba kayan abinci kamar yadda aka saba, an yanke shawarar ba mutane kuɗi domin su saye abubuwan da suka fi bukata a azumi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Sanata Abdulaziz Yari ya riga ya bayar da gudunmawar tireloli 496 na hatsi, don haka minista Mattawalle ya yanke shawarar bayar da kuɗi a wannan karon,”
Yadda aka raba kuɗin tallafin a Zamfara
A cewar Gidan-Goga, mutane 200 daga kowanne daga cikin ƙananan hukumomi 14 na jihar sun samu N100,000, wanda gaba ɗaya ya kai Naira miliyan 280.
Haka zalika, manyan jiga-jigan APC guda 24 daga ƙananan hukumomi biyar na yankin Zamfara ta Yamma sun samu N250,000 wanda gaba ɗaya ya kai Naira miliyan 30.
“Jiga-jigan APC guda 90 daga ƙananan hukumomi tara na yankunan Zamfara ta Tsakiya da Arewa sun samu N50,000, wanda gabaɗaya ya kai Naira miliyan 22.5,”

Kara karanta wannan
Bayan hallaka jama'a da karbe kudin fansa, mugun 'dan ta'adda ya gamu da karshensa
Ya ƙara da cewa akwai wasu rukuni na mutane da suka amfana da tallafin Ramadan da minista Mattawalle ya bayar, wanda ba a ambaci sunayensu ba.
Fiye da kashi 80% sun karbi tallafi a Zamfara
Gidan-Goga ya bayyana cewa fiye da kashi 80% na mutanen da aka yi niyyar ba tallafin sun riga sun karɓi kuɗinsu.
A cewarsa, mutanen ƙananan hukumomin Bakura, Gummi, Kaura-Namoda, Maradun, Shinkafi da Talata-Mafara sun riga sun karɓi tallafinsu.
Ya ce an biya mutane 100 daga kowanne daga cikin ƙananan hukumomi biyar na Tsafe, Zurmi, Bungudu, Bukkuyum da Anka, yayin da sauran da suka rage za su karɓi kuɗinsu nan gaba kaɗan.
An bukaci a cigaba da yi wa Najeriya addu'a
Gidan-Goga ya bayyana cewa har yanzu mutanen Birnin Magaji ba su karɓi tallafinsu ba saboda jinkirin mika jerin sunayen waɗanda za su amfana.
Ya yi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin Ramadan daga Minista Mattawalle da su ci gaba da yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya da cigaba.

Asali: Facebook
An fara cike fom na neman tallafin Barau
A wani rahoton, kun ji cewa an fara cike fom domin samun tallafin noma da Sanata Barau Ibrahim Jibrin ya kaddamar.
Barau Jibrin ya kaddamar da shirin ne domin tallafawa matasa su samu jarin da za su fara noma a jihohin Arewa ta Yamma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng