Ministocin Tinubu Sun Hada Kai, Ana Shirin Samawa Matasa Miliyan 5 Aiki

Ministocin Tinubu Sun Hada Kai, Ana Shirin Samawa Matasa Miliyan 5 Aiki

  • Ma’aikatun ci gaban matasa da na kwadago sun hada gwiwa don horar da matasa ta hanyar shirye-shiryen LEEP da kuma NIYA
  • Ministan matasa, Ayodele Olawande, ya ce gwamnati ta dukufa wajen rage rashin aikin yi ta hanyar koyar da sana’o’i, fasaha, da jagoranci
  • A bangarenta, karamar Ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta fadi yadda shirin zai taka rawa wajen bunkasa tattalin arziki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMa’aikatun ci gaban matasa da na kwadago a kasar nan sun hada gwiwa don samar da sababbin ayyukan yi miliyan biyar ga jama'ar Najeriya.

Za a cimma manufar ne ta shirin kwadago da koyar da sana'o'i (LEEP) da cibiyar koyar da matasan Najeriya (NIYA), wanda ma’aikatun biyu suka ce za yi amfani da su wajen koyar da sana'o'i.

Kara karanta wannan

Magoya bayan El-Rufa’i sun fara shirin birkita jam'iyyar SDP

Tinubu
Gwamnatin Tinubu na shirin samarwa matasa ayyukan yi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan yayin bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gwamnatin Tinubu ta damu da matasa” Inji Minista

Olawande ya jaddada cewa shirin shugaba Bola Tinubu na farfado da Najeriya na da cikakken kudiri na samar da sauye-sauye don bunkasa rayuwar matasa.

Tinubu
Ma'aikatun gwamnati biyu sun yi yarjejeniyar samawa matasa aikin yi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya kara da cewa yarjejeniyar da aka sanya hannu ta nuna yadda gwamnati ke daukar batun samar da aikin yi ga matasa da matukar muhimmanci.

Ya ce:

“Mun fahimci cewa mafi girman alamar nasarar mu ita ce rage adadin matasan da ke zaman kashe wando. Wannan ne dalilin da ya sa hadin gwiwarmu da ma’aikatar kwadago da samar da ayyuka ke da muhimmancin gaske."
Wannan hadin gwiwa ba alkawuri ne kawai ba ne, a’a, aiki ne za a yi Ta hanyar hada horon sana’o’i, fasaha, da jagoranci, muna tabbatar da cewa matasan Najeriya suna da kwarewar da za ta ba su damar yin fice a kasuwar aikin yi ta zamani.”

Kara karanta wannan

"Jonathan ya yi bankwana da siyasa," PDP ta magantu kan fito da shi takara

Yadda gwamnatin Tinubu za ta samar da aiki

Ministan ya kara da cewa wannan shiri zai bai wa matasa damar shiga ayyukan da ake da su a halin yanzu, sannan kuma ya zaburar da su domin su zama masu kirkirar ayyuka.

Ya ce:

“Yayin da mu ka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a yau, bari mu tabbatar da cewa mun kuduri aniyar rage rashin aikin yi, fadada damarmakin bunkasa tattalin arziki, da kuma samar da kyakkyawar makoma ga matasan Najeriya.”

A nata bangaren, karamar Ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta ce burin gwamnati shi ne karfafa karfin ma’aikatan Najeriya da fadada damarmakin samun aiki.

Ta ce:

“Yarjejeniyar da aka rattaba hannu a yau tsakanin ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi da ma'aikatar ci gaban matasa, mataki ne mai matukar muhimmanci wajen cimma wannan burin.”

Gwamnatin Tinubu za ta rage zaman kashe wando

A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa za ta samar da ayyukan yi fiye da miliyan biyu ga matasan kasar nan, musamman a ɓangaren nishaɗi da fasaha.

Kara karanta wannan

Bayan hallaka jama'a da karbe kudin fansa, mugun 'dan ta'adda ya gamu da karshensa

Ministar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arziki, Hannatu Musawa, ce ta bayyana haka, ta kuma kara da cewa gwamnati na da shirin samarwa matasa abin yi domin rage rashin aikin yi a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng