Za a Kafa Babban Kamfanin Siminti a Arewa, Mutane 45,000 za Su Samu Aiki
- Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejeniya da kamfanin MSM don gina kamfanin siminti a jihar Kebbi, wanda zai samar da tan miliyan uku duk shekara
- Sabon kamfanin zai samar da guraben ayyuka 20,000 kai tsaye da kuma 25,000 a hanyoyin da ba kai tsaye ba, wanda zai rage matsalar rashin aikin yi
- Ministan kudi, Wale Edun, ya ce kamfanin zai bunkasa kasuwanci da fitar da kaya zuwa kasashen Afirka domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Najeriya na ci gaba da daukar matakai don habaka masana’antu da fitar da kayayyaki zuwa ketare domin bunkasa tattalin arziki.
A ranar Jumu'a ne aka kulla wata muhimmiyar yarjejeniya da kamfanin MSM don gina katafaren kamfanin siminti a jihar Kebbi.

Asali: Twitter
Ma'aikatar kudi ta wallafa a X cewa, ministan kudi, Wale Edun ne ya jagoranci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar tare da wasu manyan jami’an gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda kamfanin simintin zai samar da ayyuka
Sabon kamfanin simintin da aka tsara za a gina shi a jihar Kebbi zai samar da dimbin ayyukan yi ga al’umma.
Bisa bayanan da aka tattara, mutane 20,000 ne za su samu guraben aiki kai tsaye, yayin da wasu 25,000 za su amfana ta hanyoyi daban-daban.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan katafaren kamfani zai kara habaka fannin masana’antu da rage dogaro da shigo da siminti daga kasashen waje.
A cewar jami’ai, gina kamfanin zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi, musamman ga matasa da mata a jihar Kebbi da ma sauran sassan kasar.
Za a bunkasa kasuwanci, a rika fitar da kaya
Wale Edun ya ce kamfanin yana da matsayi mai muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki da fitar da kayayyaki zuwa ketare.
Wurin da aka zaba don aikin yana kusa da iyakar Najeriya da wasu kasashen Afirka, wanda hakan zai saukaka fitar da siminti zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
Ministan kudi, Wale Edun, ya bayyana cewa aikin yana daya daga cikin manufofin shugaba Bola Tinubu na habaka kasuwanci da rage talauci a Najeriya.

Asali: Getty Images
Gwamnan Kebbi ya yaba da lamarin
Gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya bayyana aikin a matsayin wani ci gaban da zai habaka tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.
Ya ce samar da irin wadannan masana’antu zai taimaka wajen rage yawan matasan da ke zaman kashe wando tare da bunkasa sana’o’in al’umma.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta bayar da duk goyon bayan da ake bukata don ganin an kammala aikin cikin nasara.
Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa kokarinta na bunkasa harkokin masana’antu da samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya.
Tinubu zai dauki matasan Najeriya aiki
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar matasa 774 aikin gwamnati.
Matasan da aka zakulo daga kananan hukumomin Najeriya domin sa-ido a kan cibiyoyin kiwon lafiya za su samu aiki idan suka gama aikin wucin gadi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng