Mutuwa Ta Girgiza Tinubu: Babban Farfesan Jami'ar ABU Ya Rigamu Gidan Gaskiya
- Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhinin rasuwar Farfesa Kharisu Chukkol, fitaccen masanin shari’a daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria
- Marigayin ya riƙe mukamai da dama a ABU, ciki har da shugaban sashen koyar da shari’a da kuma daraktan cibiyar harkokin gudanarwa
- Shugaban ƙasa ya yaba da gudunmawar da Farfesa Chukkol ya bayar, musamman littafinsa na 1988 mai take: "Dokar Laifuffuka a Najeriya"
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya karbi rayuwar daya daga cikin manyan farfesoshin jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, jihar Kaduna.
Fadar shugaban kasa, a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Litinin ta ce shugaba Bola Tinubu ya girgiza da rasuwar Farfesa Kharisu Sufiyanu Chukkol.

Asali: Twitter
Sanarwar da aka wallafa a shafin fadar shugaban kasar na X, ta nuna cewa Farfesa Kharisu Chukkol ya rasu a ranar Lahadi a Abuja, yana da shekaru 79.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya yi alhinin rasuwar farfesan ABU
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana mika ta'aziyyarsa ga iyalai, dalibai da masu koyon ilimi a hannun fitaccen masanin shari'a, Farfesa Kharisu Sufiyanu Chukkol, wanda ya rasu ranar Lahadi da yamma a Abuja, yana da shekaru 79."
- Inji sanarwar fadar shugaban kasa.
Sanarwar ta ce Farfesa Chukkol ya kasance dan asalin garin Mayo Belwa ne da ke jihar Adamawa, kuma ya sadaukar da rayuwarsa ga harkar koyar da ilimi.
Fadar shugaban kasar ta ce:
"Farfesa Chukkol ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da ilimin shari’a a jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria. Ya kware a fannin dokokin laifuffuka.
"Ya riƙe mukamai da dama a ABU, ciki har da shugaban sashen koyarwa da ilimin Shari’a da daraktan cibiyar harkokin gudanarwa."
Abubuwan tunawa da Farfesa Chukkol
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya tuno da irin gudunmawar da Farfesa Chukkol ya bayar wajen samar da kwararrun lauyoyi a Najeriya na tsawon lokaci.
"Daga cikin wadanda Farfesa Chukkol ya koyar akwai alkalan kotun kolin Najeriya da na sauran kotuna, akwai manyan lauyoyi da ma shi kansa NSA, Mallam Nuhu Ribadu."
- Inji sanarwar fadar shugaban kasa.
Shugaban kasar ya kuma yi bayani kan irin tarin abubuwan alheri a fannin ilimi da marigayin ya bari, musamman littafin da ya buga a 1988 mai taken: "Dokar laifuffuka a Najeriya."
Sanarwar ta ce wannan littafi har gobe yana ci gaba da zama tushen bincike ga masana da masu gudanar da harkokin shari'a a kasar nan.
Tinubu ya aika sako ga iyalan marigayin

Asali: Twitter
Bai tsaya a nan ba, Shugaba Tinubu ya ce koyarwar Chukkol ta shafi har 'ya'yansa, ciki har da Abdulkarim Chukkol, tsohon mukaddashin shugaban EFCC.
Shugaban kasar ya bukaci iyali, dalibai da duk wadanda alherin rayuwar Farfesa Chukkol ya shafa su zamo masu koyi ga koyarwarsa da kuma girmama ayyukan da ya yi.

Kara karanta wannan
Babban farfesa a Najeriya ya yanke jiki ya fadi ana azumi, ya mutu a hanyar asibiti
Tinubu ya kuma yi addu'ar Allah ya lullube marigayi Farfesa Kharisu Sufiyanu Chukkol da rahamarsa ya kuma ba shi salama a kwanciyar kabarinsa.
Abdulkarim Chukkol ya zama shugaban EFCC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bayan dakatarwar da shugaban kasa ya yi wa Abdulrasheed Bawa, EFCC ta sanar da sabon shugaban rikon kwarya.
An tabbatar da Abdulkarim Chukkol a matsayin wanda zai maye gurbin Bawa har zuwa lokacin da shugaban kasar zai nada sabon shugaba a lokacin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng