Gwamna Ya Fadi Dalilin Gyara da Gina Coci yayin Ta'aziyyar Rasuwar Malamin Musulunci
- Gwamna Bala Mohammed ya bayyana dalilin da yasa gwamnatinsa ke gina wa da gyaran coci-coci a jihar Bauchi, domin tabbatar da adalci ga kowa
- Gwamna Bala ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, bisa rasuwar Janar Useni da Sheikh Hassan Jingir
- Gwamnan ya ce suna gina coci domin Kiristoci ma 'yan jihar ne, suna da hakkinsu kamar kowa inda ya jaddada muhimmancin hadin kai
- Ya yabawa Gwamnan Filato bisa saka kowa da kowa a mulkinsa, yana mai cewa abin da ya shafi jihar ya shafe su su ma a Bauchi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya ziyarci gwamnan Filato domin yi masa ta'aziyyar rasuwar Sa'idu Hassan Jingir.

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda
Gwamna Bala ya bayyana dalilin da yasa gwamnatinsa ke ginawa da gyaran coci-coci a fadin jihar Bauchi.

Asali: Facebook
Mene musabbabin gyara da gina coci a Bauchi?
Sanata Mohammed ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ta'aziyya kan rasuwar Janar Jeremiah Useni da Sheikh Hassan Jingir a birnin Jos, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar gwamnan, yana gina coci domin Kiristoci ma suna da hakki a matsayin 'yan jihar Bauchi kamar kowane dan kasa.
Gwamna Bala ya ce:
“Kai kana gyara masallaci a matsayin gwamna, ba a taba hakan ba, Mu ma muna ginawa da gyaran coci domin 'yan jihar ne.
Yayin da yake jajanta wa Gwamna Mutfwang, Sanata Mohammed ya ce:
“Sheikh Hassan Saeed Jingir ya kasance malami nagari wanda za a dade ana tunawa da shi.”
“Ina sauraron wa’azinsa. Ya zo Bauchi sau da dama yana wa’azi, Ya taimaka sosai wajen yada addinin Musulunci a duk faɗin ƙasa.”
“Muna jin daɗin irin mulkin hadin kai da kake yi, Mun ji ana cewa kana tafiya da kowa, Wannan abin farin ciki ne a gare mu.”

Asali: Facebook
Gwamna ya sha alwashin inganta rayuwar al'ummar jiharsa
Gwamna Bala Mohammed ya ba Caleb Mutfwang tabbacin ci gaba da ayyukan alheri a matsayin jihohi da ke makwabtaka.
Gwamnan na daga cikin sauran gwamnonin Arewa da suka sha suka bayan rufe makarantu a jihohinsu saboda azumin watan Ramadan da ake yi yanzu.
Sanata Bala ya kara da cewa:
“Ina tabbatar maka cewa mu a matsayin makwabtan ku, za mu ci gaba da bayyana ayyuka nagari da kake yi."
Sanata Ningi zai tsaya takarar gwamna
Mun ba ku labarin cewa Sanata Ahmed Abdul Ningi ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Bauchi a zaben shekarar 2027 karkashin PDP.
Sanatan ya bayyana haka ne yayin ganawa da shugabannin jam’iyyar PDP a karamar hukumar Ganjuwa wacce ke karkashin mazabarsa.
Sanata Ningi ya ce ba yana son shahara ba ne, amma yana da burin ci gaba da yi wa jama’a hidima da cikakken nauyi da girman mukami a Bauchi.
Dan siyasar ya jaddada cewa shi dan PDP ne tun daga kafuwar jam’iyyar, kuma yana da burin tabbatar da cewa jam’iyyar ta ci gaba da mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng