Ramadan: Gwamna Ya Rufe Dukkanin Makarantun Jiharsa na Tsawon Mako 5

Ramadan: Gwamna Ya Rufe Dukkanin Makarantun Jiharsa na Tsawon Mako 5

  • Gwamnatin Bauchi ta sanar da rufe makarantu na gwamnati da na masu zaman kansu na tsawon makonni biyar gabanin Ramadan
  • Sanarwar ta shafi makarantun firamare har zuwa na gaba da sakandare, yayin da aka ce hutun na cikin jadawalin karatun 2024-2025
  • To sai dai kuma, wasu iyaye sun bayyana damuwa cewa hutun Ramadan mai tsawo zai shafi karatun yara, tare da rokon a duba matakin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnatin Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkanin makarantu na gwamnati da ma na masu zaman kansu da ke a fadin kananan hukumomin jihar.

Gwamnatin jihar ta ce ta yanke shawarar rufe dukkanin makarantun na tsawon makonni biyar domin shirin azumin Ramadan na shekara ta 1446.

Gwamnatin Bauchi ta yi magana da ta ba dalibai hutun makonni 5 na Azumi
Gwamnatin Bauchi ta ba daliban jihar hutun makonni 5 na Ramadan. Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Facebook

Za a rufe dukkanin makarantun Bauchi

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fitar da sanarwa kan ganin watan Ramadan na 2025

Wannan sanarwar tana cikin jadawalin karatun shekarar 2024/2025 na gwamnatin jihar, wanda aka amince da shi, kamar yadda Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Juma'a, jami'in sashen labarai na ma'aikatar ilimin jihar, Jalaludeen Maina, ya bayyana wa kamfanin NAN cewa an riga an shigar da hutun a cikin jadawali tun kafin wannan lokaci.

Malam Jalaludeen Maina ya kara da cewa, rufe makarantun zai fara aiki daga 1 ga watan Maris har zuwa 5 ga Afrilun 2025.

Lokacin da za a dawo karatu a Bauchi

Sanarwar ta shafi dukkanin makarantun ilimi a jihar, wanda ya hada da makarantu na gwamnati da na masu zaman kansu, daga na firamare zuwa na sakandare, har ma da manyan makarantu.

Maina ya tabbatar da cewa:

"Eh, za mu rufe dukkanin makarantu a jihar, wannan yana cikin jadawalin karatun 2024/2025 da aka amince da shi.
Wannan yana nufin cewa ɗalibanmu ba za su yi azumin Ramadan a makaranta ba."

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Jami'in ya bayyana cewa hutun makonni biyar ya shafi azumin Ramadan, kuma bayan kammala azumin, ɗaliban za su dawo makaranta don ci gaba da karatunsu.

Iyaye na korafin hutun mako 5 a Bauchi

Iyayen yara sun yi korafi yayin da gwamnatin Bauchi ta ba da hutun makonni 5
Iyayen yara sun roki gwamnatin Bauchi ta rage hutun makonni 5 na azumi da ta ba da. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sai dai, wasu daga cikin iyaye a jihar sun nuna damuwa game da tasirin wannan hutu mai tsawo a ci gaban ilimin 'ya'yansu.

Wata mata, Misis Sunita Joseph, ta bayyana takaicinta game da wannan mataki, tana mai cewa lokaci mai tsawo na hutu na iya sa yara su manta da abin da suka koya kafin hutun.

"Me zai sa hutun Ramadan ya zama mai tsawo haka? Watakila yaran sun fara mantawa da abubuwan da suka koya kafin hutun,"

- Misis Joseph.

Haka kuma, Ismail Raji ya nemi gwamnatin jihar ta sake duba wannan mataki, yana mai cewa zai kara tabarbarewar lamurran yaran da ba sa zuwa makaranta.

Mohammed Isa, wanda ya nuna damuwarsa game da wannan al'amari, ya tunatar da gwamnatin jihar cewa Bauchi tana daga cikin jihohin da ke da yawan yara da ba sa zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum zai koya wa talakawa neman na kai a jihar Borno

Isa ya ce akwai bukatar gwamnati ta fito da shirye-shirye da ayyuka da za su karfafawa iyaye gwiwa wajen tura 'ya'yansu makaranta ba wai ba da hutu na dogon lokaci ba.

'Dan majalisa ya rabawa mutane 5000 tallafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hon. Usman Zannah, ɗan majalisar Kaga/Magumeri/Gubio, ya ba da tallafi ga al'ummarsa domin rage wahalhalu, musamman a lokacin Ramadan.

Tallafin ya haɗa da shinkafa, sukari, taliya da kudade, wanda Zannah ya ce yana bayarwa kowane lokaci domin al'umma su yi azumi cikin walwala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.