"An Samu Ci Gaba": Matakin da Mutane Suka Dauka don Kawo Karshen Harin 'Yan Bindiga
- An hau kan teburin sulhu tsakanin ƴan bindiga da mutanen ƙananan hukumomin Jibia, Safana da Batsari a jihar Katsina
- Shugabannin al'umma sun jagoranci cimma yarjejeniya da ƴan bindiga domin a samu zaman lafiya a wadannan garuruwa
- Babu hannun gwamnatin jiha kai tsaye a cikin sulhun domin ta sha nesanta kanta da tattaunawa ko sulhu da ƴan bindiga
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Shugabannin al’umma a ƙananan hukumomin Jibia, Batsari da Safana na jihar Katsina sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ƴan bindigan da ke addabar garuruwansu.
Mazauna yankin sun ce an kammala sabuwar tattaunawar zaman lafiya tsakanin shugabannin Jibia da ƴan bindiga a ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu, bayan an yi makamancin hakan a Batsari da Safana.

Asali: Original
Sun bayyana cewa wakilan sojoji, DSS, ƴan sanda, ƙungiyoyin sa-kai, masu gadin gari, sarakunan gargajiya da jami’an ƙananan hukumomin sun halarci tattaunawar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe mahaddacin Kur'anin da suka sace a Katsina? An gano gaskiya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka yi sulhu da ƴan bindiga?
An samu labarin cewa Audu Lankai, wani sanannen hatsabibin ɗan bindigan yankin ne ya fara wannan shirin na zaman lafiya, yana mai bayyana cewa ya gaji da rikicin da aka daɗe ana yi.
Wata sahihiyar majiya a Jibia ta bayyana cewa shugabannin al'ummar yankin ne suka jagoranci shirin.
"Gwamnatin jiha ba ta da hannu kai tsaye a cikin wannan shirin. Gwamna ya sha nanata cewa ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba sai dai idan sun miƙa wuya."
"Amma a wannan karon, shugabanninmu sun gana da wani babban jami’in gwamnati, kuma sun ba mu goyon baya muddin za a yi zaman lafiyar bisa sharuɗɗanmu."
"Hatsabibin ɗan bindiga, Audu Lankai, shi da kansa ne ya nemi a yi zaman sulhu, yana mai cewa ya gaji da wannan rikici."
“Ya tuntuɓi ɗaya daga cikin shugabanninmu, bayan tattaunawa, muka amince da cewa za mu haɗu a wannan ranar Juma’ar."

Kara karanta wannan
Ana daf da cafke hatsabibin ɗan bindiga da ake nema ruwa a jallo bayan kama hadiminsa
"Haka kuma, mun yarda da cewa za a ci gaba da tattaunawar bayan Sallah, idan kowa ya kiyaye sharuɗɗan da aka gindaya."
- Wata majiya
Waɗanne sharuɗɗa aka kafawa ƴan bindigan?
Daga cikin sharuɗɗan da al’ummomin Jibia suka kafa akwai:
- Daina kai hare-hare kan matafiya a manyan hanyoyin Jibia-Katsina, Jibia-Batsari da Jibia-Gurbi.
- Daina farmakar ƙauyuka da sace mutane, ba wa manoma da mazauna yankin damar yin harkokinsu ba tare da tsoro ba.
- Sakin mutanen da aka yi garkuwa da su tare da miƙa makamai.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu, an sako mutane 11 da aka yi garkuwa da su, sannan ƴan bindigan sun miƙa bindigogi guda biyu.
Majiyar ta kuma ce ƴan bindigan sun bukaci a bar su suna shiga cikin al’umma ba tare da barazana ga rayuwarsu ba.
Ƙwace makamansu a hankali a hankali, saboda suna bukatar kare kansu daga ƙungiyoyin ƴan bindiga masu adawa da su da kuma kare al’ummominsu daga ƴan bindigan da ba su shiga yarjejeniyar ba.
Kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu
Mazauna ƙauyukan da abin ya shafa sun bayyana jin daɗinsu, suna mai cewa wannan shirin zaman lafiya da al’umma suka ɗauki nauyinsa ya fara haifar da sakamako mai kyau.
Sun bayyana cewa yankunan da a baya aka riƙa jin tsoro a shiga sun fara komawa kamar yadda suke, kuma al’umma sun fara ci gaba da harkokinsu kamar da.
Za a sake zama bayan Sallah
Legit Hausa ta tuntuɓi mataimakin kwamitin tsaron na Jibia, Nasiru Jibia wanda ya bayyana za a ci gaba da tattaunawa bayan Sallah.
"Mun tattauna da su, mun kuma miƙa musu sharuɗɗanmu, zuwa bayan Sallah za a sake zama domin mu ga a ina aka kwana kan yarjejeniyar."
"Alhamdulillah abubuwa yanzu sun fara yin sauƙi, hankula na ta ƙara kwanciya."
- Malam Nasir Jibia
Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Ƴan bindiga a yayin harin sun kashe mutum ɗaya kafin su tsere zuwa cikin daji bayan dakarun sojoji sun kawo ɗaukin gaggawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng