Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram

  • Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • Sojojin sun yi nasarar kashe wani babban kwamandan ƴan ta'addan a wani farmaki mai zafi da suka kai kan maɓoyarsu
  • Jami'an tsaron sun hallaka ƴan ta'adɗa masu yawa tare da ƙwato tarin makamai bayan sun yi musu korar kare

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe babban kwamandan Boko Haram, Abba Alai (Amirul Khahid na Alafa), da ƴan ta'adda da dama a cikin hare-haren hadin gwiwa a Garin Fallujah da Gwoza, jihar Borno.

Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram a Borno
Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram a Borno Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun zo da sabon ta'addanci wajen sace mutane a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji ƴan Boko Haram

Sojojin sun kai farmakin kakkaɓe ƴan ta'addan ne bayan samun ingantaccen bayanan sirri.

An kai farmakin ne kan wata maɓoyar ƴan ta'adda mai tsaro sosai inda masu tayar da ƙayar baya ke taruwa don kai hare-hare.

Sojojin sun kai zazzafan hari, inda suka yi musayar wuta ba ƙaƙƙautawa tare da ƴan ta'addan.

Sakamakon yin amfanin da sojoji suka yi da makaman da suka fi na ƴan ta'addan, tsagerun sun yi ƙoƙarin tserewa amma sun samu mummunan asarar rai.

Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Abba Alai, wani shahararren kwamandan da aka san shi da shirya munanan hare-hare a yankin.

Makaman da aka ƙwato daga farmakin sun haɗa da, bindigar AK-47 guda ɗaya, jigidar bindigar AK-47 guda ɗaya, harsasai 23 na musamman masu kaurin milimita 7.62, na'urar rediyo guda ɗaya, babbar bindigar DSHK, babur guda ɗaya da magunguna.

Ƴan Boko Haram sun gwabza da sojoji

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun hallaka 'yan sa kai a Kebbi

A wani farmakin na daban a yankin ƙaramar hukumar Gwoza, sojojin da aka tura don hana ƴan ta'adda tserewa daga Dajin Sambisa, sun yi artabu da miyagu a ƙauyen Gobara.

Musayar wutar ya sanya ƴan ta'addan sun tsere inda aka ƙwato makaman da suka haɗa da, harsasai 57 masu kaurin 12.7mm, harsasai 30 na musamman masu kaurin 7.62mm, jigidar bindigar AK-47 guda uku.

Sauran sun haɗa bindiga ƙirar gida guda ɗaya da kuma bindigogi guda biyu da ake zaton ana amfani da su wajen koyar da ƴan ta'adda.

A yayin farmakin, sojojin sun kuma ceto wata tsohuwa da ƴan ta'addan suka tsare har tsawon shekaru 10.

Babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yaba wa sojojin bisa jajircewar su wajen kawar da yan ta'adda.

Ƴan Boko Haram sun kai hari a Adamawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Azumin Ramadan: Atiku Abubakar ya tura muhimmin sako ga gwamnatin tarayya

Ƴan ta'addan sun ƙona gidaje, makarantu da wuraren ibada a hare-haren da suka kai a ƙaramar hukumar Hong ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng