Dakarun Sojoji Sun Kai Dauki bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Mutane, Sun Samu Nasara
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Katsina da wasu garuruwa ke cikin barazana
- Sojojin na rundunar Operation Fansan Yanma sun daƙile yunƙurin yin garkuwa sa mutane da wasu ƴan bindiga suka yi a ƙaramar hukumar Kankia
- Ƴan bindigan dai sun kai hari ne a garin Mashayayya inda suka harbi wani mutum tare da ƙwace kuɗaɗe da wayoyin mazauna yankin
- Da samun labarin harin, sai dakarun sojoji suka bi bayan ƴan bindigan waɗanda suka kawo harin na ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fasan Yanma sun samu nasara kan wasu ƴan bindiga a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun iya daƙile yunƙurin yin garkuwa da mutane da wasu ƴan bindiga suka yi a ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kuɓutar da mutum 1
Dakarun sojojin sun kuɓutar mutum guda yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto wasu mutum biyu da aka sace.
Majiyoyin sirri sun bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Juma'a, 7 ga watan Maris, 2025, lokacin da ƴan bindiga suka afkawa garin Mashayaya.
Ƴan bindigan sun harbe wani mutum mai suna Lado Mekaji a kafafuwansa guda biyu, sannan suka ƙwace wayoyi da kuɗaɗe daga hannun mazauna garin.
Daga nan, ƴan bindigan suka zarce zuwa garin Kolawa, suka yi garkuwa da wani namiji mai suna Bello da wata mace mai suna Aisha.
Da samun labarin harin, jami’an tsaro, ciki har da sojojin Operation Fansan Yanma tare da ƴan banga na yankin, suka ɗauki matakin gaggawa.
Jami'an Sojoji sun bi bayan ƴan bindiga
Jami'an tsaron sun bi sahun ƴan bindigan da nufin ceto mutanen da suka sace.
An samu nasarar ceto Lado Mekaji, kuma an kai shi asibiti don samun kulawa. Jami'an tsaron suna kuma ci gaba da ƙoƙarin gano inda Bello da Aisha suke don kuɓutar da su.
Jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen sintiri da kai farmaki a yankin don gano maboyar ƴan bindigan da hana aukuwar ƙarin hare-hare.
Ana sa ran waɗannan matakan za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram masu tayar da ƙayar baya a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram aƙalla guda tara bayan sun kai musu farmaki a maɓoyarsu.
Sojojin a yayin artabun sun hallaka kwamandan Boko Haram wanda shi ne babban mai haɗa bama-bamai na ƙungiyar.
Jami'an tsaron sun kuma samu nasarar ƙwato makamai masu tarin yawa daga hannun ƴan ta'addan na Boko Haram.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng