Majalisa Ta Tasamma Taimakon Matasan Najeriya, Ta ba NCC Umarnin Rufe Shafukan Batsa

Majalisa Ta Tasamma Taimakon Matasan Najeriya, Ta ba NCC Umarnin Rufe Shafukan Batsa

  • Majalisar Wakilai ta Najeriya ta umarci Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) da ta tabbatar da rufe dukkan shafukan batsa a kasar nan
  • Wannan ya biyo bayan kudirin da dan majalisa daga jihar Katsina, Hon. Dalhatu Tafoki, ya gabatar kan illar ziyartar shafukan ga matasa
  • Hon. Tafoki ya ce akwai wasu kasashen duniya da su ka haramta wanzuwar irin shafukan da ke tallata badala a tsakanin jama'arsu
  • Majalisar ta amince da koken takwaransu, ta kuma bukaci a hukunta duk masu ba da sabis na intanet da suka ki rufe damar shiga shafukan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMajalisar wakilan Najeriya ta umarci Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) da ta tabbatar da rufe dukkanin shafukan batsa a kasar.

Kara karanta wannan

Yaki da zaman banza: Tinubu na shirin samar da ayyuka ga matasa miliyan 10

Majalisar ta bukaci hukumar NCC da ta tilasta dukkan masu ba da sabis na intanet su toshe ire-iren wadannan shafuka da ke ba matasa damar shiga shafukan da ake wallafa batsa.

Majalisa
Majalisar wakilai ta damu da yawan amfani da shafukan batsa a Najeriya Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Hon. Dalhatu Tafoki, dan majalisa daga Jihar Katsina mai wakiltar Faskari/Sabuwa/Kankara, ne ya dauki nauyin gabata da kudirin a zaman da aka yi a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa na son inganta rayuwar matasan Najeriya

Jaridar Punch ta wallafa cewa a yayin gabatar da kudirin, Hon. Tafoki ya jaddada cewa batsa a intanet babbar matsala ce da ke kara kamari a duniya.

Yan majalisa
Majalisa ta umarci NCC ta rufe dukkanin shafukan badala a Najeriya Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Ya bayana damuwa a kan yadda Najeriya ba ta dauki matakan da suka dace don shawo kanta matsalar da ke kara kamari a tsakanin matasanta ba.

Dan majalisa ya ce Najeriya ta na bin addini

A cewar dan majalisar jihar Katsina, Najeriya kasa ce mai bin addini sosai inda manyan addinai ke yin hani da kuma haramta tsiraici da batsa.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha: Shugaban Majalisa, Akpabio ya dira kan ƴan Najeriya

Kamar yadda PR Nigeria ta rahoto, Hon. Dalhatu Tafoki, ya kara da cewa:

"Najeriya kasa ce mai bin addini sosai, kuma duk manyan addinan da ke kasar na haramta tsiraici da batsa a kowane irin yanayi.
Haka kuma, a lura cewa kasashe da dama a Asiya, Afirka da Gabas ta Tsakiya sun kafa dokoki da ke haramta batsa a yankunansu.

'Dan majalisa ya fadi illar shafukan batsa

A cewarsa, kallon batsa na iya haddasa zina, karuwanci da sauran matsalalin da su ke keta mutuntaka da dan adam mai hankali.

Ya ce mashahuran masana kimiyyar kwakwalwa da zamantakewa sun yi gargadi kan illolin da ke tattare da kallon batsa, ciki har da matsalolin tunani, zamantakewa da kwakwalwa.

’Yan majalisa sun amince da kudirin

Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya nemi a kada kuri’ar murya a kan kudirin, kuma ’yan majalisa suka amince da shi.

Majalisar ta umarci hukumar NCC da ta sanya takunkumi ga duk masu ba da sabis na intanet da suka ki bin wannan umarni, tare da tabbatar da cewa an rufe shafukan da ke yada badala.

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

Majalisa ta haramtawa CBN harajin ATM

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dakatar da sabon tsarin harajin ATM tare da dawo da damar cire kuɗi kyauta a ATM.

Wannan mataki ya biyo bayan kokn 'yan Najeriya bayan sanarwar da CBN tafitar a kwanan nan, inda bankin ya ƙara yawan kuɗin da ake cirewa ‘yan Najeriya idan sun yi amfani da ATM.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng