Majalisa Ta Ji Kukan Ƴan Najeriya, An Hana CBN Ƙaƙaba Haraji kan Amfani da ATM

Majalisa Ta Ji Kukan Ƴan Najeriya, An Hana CBN Ƙaƙaba Haraji kan Amfani da ATM

  • Majalisar wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya da ya dakatar da sabon tsarin cire wa 'yan Najeriya kudi idan sun yi aiki da ATM
  • Marcus Onobun (PDP, Edo) ya jagoranci kudirin da ya bukaci dakatar da tsarin, yana cewa zai kara jefa ‘yan Najeriya a mawuyacin hali
  • Sabon tsarin na CBN yana bukatar ‘yan Najeriya su biya haraji mai yawa yayin da suka cire kudi daga ATM da ba na bankinsu ba a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta umarci bankin CBN da ya dakatar da sabon tsarin harajin ATM da kuma dawo da damar cire kuɗi kyauta a ATM.

Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwar CBN ta kwanan nan, inda ya tsaurara harajin amfani da ATM, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha: Shugaban Majalisa, Akpabio ya dira kan ƴan Najeriya

Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga aiwatar da sabon tsarin cire kudi ta ATM
Majalisar wakilai ta hana CBN cirar kudi daga masu amfani da ATM da ba bankinsu ba. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Dan majalisa ya nemi a takawa CBN Burki

Majalisar ta ba babban bankin wannan umarni ne bayan karbar wani kudiri na gaggawa da Hon. Marcus Onobun (PDP, Edo) ya gabatar, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Marcus Onobun, a cikin kudurin, ya bukaci majalisar ta umarci CBN ta dakatar da wannan tsari har sai an tattauna da kwamitocin da suka dace.

Yayin da yake gabatar da kudirin, Onobun ya ce:

"Wannan sabon tsarin ya kara yawan kudin da ake zararwa 'yan Najeriya idan sun je cire kudi ta ATM tare da cire damar cire kudi kyauta, wanda zai kuntata ‘yan kasar."

'Dan majalisa ya soki sabon tsarin CBN

A cewarsa, an sabunta sashi na 10.7 na dokar CBN kan kudaden bankuna a 2019, inda aka rage kudin harajin cire kudi ta ATM daga N65 zuwa N35.

Ya bayyana cewa bisa sabon tsarin CBN:

"Masu cire kudi ta ATM na bankinsu za su yi hakan kyauta. Amma, idan abokin hulda ya cire kudi daga ATM na wani bankin da ba nasa ba, zai biya N100 kan N20,000.

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

"Idan mutum ya cire kudi daga ATM da ke wajen harabar banki, kamar a kasuwanni ko wuraren taruwar jama’a, zai biya N100 ko kuma N500."

A cewar Onobun, wannan sabon tsarin na CBN zai kara jefa 'yan Najeriya cikin wahala, wadanda dama suke fama da hauhawar farashi, tsadar mai da karin kudin wutar lantarki.

Majalisa ta umarci CBN ta dakatar da sabon tsari

Majalisar wakilai ta dauki mataki da CBN ya kara kudin da ake cirewa yayin cirar kudi a ATM
Majalisar wakilai ta shiga tsakanin CBN da 'yan Najeriya. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

'Dan majalisar ya kuma ce yawan harajin da bankuna ke zara yana shafar jin dadin tattalin arzikin mutane, tare da hana su iya biyan bukatunsu na yau da kullum.

Hon. Onobun ya kuma yi gargaɗi cewa karin kudin cire kudi ta ATM zai hana masu karamin karfi yin amfani da na'urorin banki ko kuma bankin gaba daya.

"Wannan ya saba da kudirin CBN na fadada harkokin hada-hadar kudi. Maimakon a saukaka, wannan mataki zai sa mutane su kauracewa bankuna," inji dan majalisar.

Saboda haka, majalisar ta bukaci CBN da ya dakatar da aiwatar da wannan sabon tsari nan take, tare da ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun dura Zamfara, sun dauki alhakin kai harin da ya kashe mutane 11

Dokar bankin CBN kan cire kudi ta ATM

A wani labarin, mun ruwaito cewa, CBN ya tabbatar da cewa za a cire N100 a matsayin haraji ga duk wanda ya cire kudi ta ATM na wani banki, ko da kuwa kasa da N20,000 ne.

Babban Bankin Najeriya ya yi wannan karin haske bayan da farko ya bayyana cewa harajin zai shafi wadanda ke cire N20,000 ko fiye ta ATM.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.