Sheikh Sani Yahaya Jingir Ya Ɗauki Gwamna 1, Ya Kwararo Masa Yabo kan Abubuwa 3

Sheikh Sani Yahaya Jingir Ya Ɗauki Gwamna 1, Ya Kwararo Masa Yabo kan Abubuwa 3

  • Shugaban Izalar Jos, Sani Yahaya Jingir ya yabawa gwamnan Filato, Caleb Mutfwang bisa kokarin da yake a muhimnan ɓangarori uku
  • Sheikh Jingir ya ce gwamnan yana matuƙar kokari wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da kuma gudanar da mulkin adalci a Filato
  • Malamin ya yi wannan yabon ne da Gwamna Mutfwang ya kai maza ziyarar ta'aziyya bisa rasuwar Sheikh Sa'eed Hassan Jingir

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, Plateau - Shugaban Majalisar Malamai na Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus-Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yaba wa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang.

Sheikh Jingir, shugaban Izala mai hedkwata a Jos ya yabawa gwamnan ne bisa jajircewarsa wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai, da mulki na adalci a Filato.

Sheikh Jingir da Caleb Mutfwang.
Sheikh Jingir ya yaba wa gwamnan Filato kan kokarin samar da zaman lafiya da haɗin kai Hoto: Sheikh Sani Yahaya Jingir, Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Babban malamin ya yi wannan yabo ne yayin da Gwamna Mutfwang ya kai masa ziyarar ta’aziyya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An ba gwamna lambar yabon 'Khadimul Qur'an' saboda hidimtawa littafin Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Mutfwang ya je ta'aziyya ga Sheikh Jingir da sauran shugabannin JIBWIS bisa rasuwar mataimakin shugaban ƙungiyar na biyu, Sheikh Saeed Hassan Jingir.

Sheikh Jingir ya yabawa Gwamna Mutfwang

Malam Sani Yahaya ya bayyana Gwamna Mutfwang a matsayi shugaban mai hangen nesa, mai juriya kuma abin misali a fagen kyautata zamantakewa.

Sheikh Jingir ya jinjinawa gwamnan bisa sadaukar da kansa wajen kula da marasa galihu da kuma samar da ci gaba ga al’umma a jihar Filato.

Ya jaddada cewa mulkin gwamnan ya taimaka matuƙa wajen ƙarfafa haɗin kai da gina amana tsakanin jama’a ta hanyar kyakkyawan shugabanci da ayyukan raya ƙasa.

Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa, masu mulki da wadanda suka sauka daga mukami, da su haɗa kai domin samar da ci gaba a jihar Filato.

Jingir ya roki mutane su goyi bayan Tinubu

Har ila yau, ya roƙi al’umma su goyi bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu domin samar da daidaito a ƙasa da inganta rayuwar al’ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara Kamari, jam'iyyar APC ta buƙaci gwamna ya yi murabus cikin sa'o'i 48

A nasa jawabin, Gwamna Caleb Mutfwang ya mika ta’aziyyarsa ga shugabannin JIBWIS watau Izala da dukkan al’ummar Musulmi bisa rasuwar Sheikh Saeed Hassan Jingir.

Gwamnan ya yaba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen samar da zaman lafiya, juriya, da adalci a faɗin Najeriya.

Sa'eed Jingir.
Gwamna Caleb Mutfwang ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar Sheikh Sa'eed Jingir Hoto: Sheikh Sani Jingir
Asali: Facebook

Gwamna ya gode wa ƙungiyar Izala

Gwamnan ya bukaci al’ummar Musulmi su ci gaba da aiki tukuru kuma su yi koyi da kyawawan dabi’un marigayin, musamman na gaskiya da taimakon jama’a.

Bugu da ƙari, Mai girma Gwamna Mutfwang ya gode wa ƙungiyar Izala da al’ummar Musulmi bisa irin goyon bayan da suke ba wa gwamnatinsa.

Ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa na kokarin yin adalci da daidaito domin kowane ɗan jihar Filato ya ci moriyar shirye-shiryen da ta ɓullo da su na ci gaba.

Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga Izala

A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar mataimakin shugaban Izalar Jos, Sheikh Sa'eed Hassan Jingir.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi dalilin gyara gyara da gina coci yayin ta'aziyyar rasuwar malamin Musulunci

Tinubu ya ce marigayin ya kasance mutum mai kwarewa da ilimi mai zurfi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimin Musulunci da shiryar da al’umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262