Yadda Rasuwar Sheikh Saidu Jingir Ta Girgiza Gwamnoni da Malaman Najeriya
- Shahararrun malamai da ‘yan siyasa a Najeriya sun nuna alhinin rasuwar fitaccen malamin Izala, Sheikh Saidu Hassan Jingir, tare da mika ta’aziyyarsu ga iyalansa
- Malamai irin su Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Sheikh Isa Ali Pantami sun yi addu’a, suna roƙon Allah ya gafarta masa ya kuma sanya Aljannah ce makomarsa
- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, da tsohon gwamnan Gombe, Sanata Ibrahim Dankwambo, sun jajanta wa iyalan marigayin da dukkan al’ummar Musulmi
- Wani dan agaji a jihar Gombe ya zantawa Legit yadda suka yi mu'amala da malamin a shekarun da ya shafe yana tafsiri a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - An ji Allah Ya yi wa mataimakin shugaban malaman Izala na ƙasa na biyu, Sheikh Saidu Hassan Jingir rasuwa.
Rasuwarsa ta girgiza al’umma, musamman ‘yan kungiyar Izala, inda aka rika nuna alhini da jimami a kafafen sada zumunta.

Asali: Facebook
Shahararrun malamai da manyan ‘yan siyasa sun wallafa sakonnin ta’aziyya, kamar yadda Sheikh Aminu Daurawa ya wallafa ta'aziyarsa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamai sun yi addu’a ga Sheikh Saidu Jingir
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana Sheikh Jingir a matsayin babban malami da ya bayar da gudunmawa mai yawa a addini.
Sheikh Daurawa ya rubuta:
"Allah yaji kansa, ya sa Aljannah ta zama makoma a gare shi."
Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya nuna alhinin sa tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da almajiransa.
Sheikh Pantami ya wallafa a Facebook cewa:
"Muna ta’aziyya zuwa ga iyalansa, yan'uwansa, da Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir da dukkan almajiran malam."
'Yan siyasa sun yi ta'aziyyar Sheikh Jingir
Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya mika ta'aziyya ga iyalan malamin.
Mai magana da yawun gwamnan jihar ya wallafa a Facebook cewa rasuwar malamin babban rashi ne ga addini.
Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, ya wallafa a Facebook cewa rasuwar Sheikh Jingir babban rashi ne ga al’ummar Musulmi.
Ya rubuta cewa:
"Allah gafarta masa, ya sa Aljannah ce makomarsa, Allah kuma ya kyautata bayansa da namu karshen."
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana marigayin a matsayin jigo a kungiyar Izala da da’awa wanda rayuwarsa cike take da darussa.
Sanata Bala Mohammed ya ce:
"Kasancewar sa fitaccen malami me da’awa, rayuwarsa cike take da kyawawan dabi’u da tsantsar Tauhidi."

Asali: Facebook
An roƙi Allah ya gafarta wa Sheikh Jingir
Gwamnan Bauchi ya jajanta wa iyalan Sheikh Jingir, kungiyar Izala, da daukacin al’ummar Musulmi bisa wannan babban rashi.
Gwamnan ya wallafa a Facebook cewa:
"Muna roƙon Allah ya kyautata bayan sa, ya gafarta masa, ya kuma cika mu da rahamarSa."
Haka zalika, sauran malamai da ‘yan siyasa sun bukaci al’umma da su ci gaba da yin addu’a ga marigayin.
Sun bayyana cewa Sheikh Jingir ya bar gagarumar gudunmawa da za a ci gaba da amfana da ita a duniya da Lahira.
Legit ta tattauna da dan agaji
Wani dan agajin Izala, Sani Abdullahi ya zantawa Legit cewa malamin yana musu mu'amala mai kyau tare da karfafa su a shekarun baya.
Dan agajin ya ce:
"Malam yana da kirkiki sosai. Yana wasa da dariya da mu. Yana mana kallon kamar 'ya'yansa ne, shi yasa za ka ji yana ce mana 'ya'yansa a wajen karatu."
Malami ya soki gwamnoni kan hutun azumi
A wan rahoton, kun ji cewa wani malamin addini a jihar Edo ya soki matakin da wasu gwamnoni suka dauka na rufe makarantu.
Malamin ya yi magana ne yayin da gwamnonin suka ce ba gudu ba ja da baya a kan matakin da suka dauka na rufe makarantu a watan Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng