Abin da Tinubu Ya Fada kan Rasuwar Shugaba a Izala, Sheikh Saidu Jingir

Abin da Tinubu Ya Fada kan Rasuwar Shugaba a Izala, Sheikh Saidu Jingir

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga al'ummar Musulmi kan rasuwar Sheikh Saidu Hassan Jingir
  • Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagoran addini wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimin Musulunci
  • Sannan ya roki Allah SWT Ya gafarta Sheikh Saidu Hassan Jingir kurakuransa tare da ba shi gidan Aljannah Firdaus a gobe kiyama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An shiga jimami a fadin Najeriya sakamakon rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Saidu Hassan Jingir.

Sheikh Jingir wanda ya kasance mataimakin shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala mai hedkwata a Jos kuma ya rasu ne a ranar Alhamis.

Tinubu
Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Saidu Jingir. Hoto: Hamza Muhammad Sani|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da shugaban kasar ya yi ne a cikin wani sako da fadar shugaban kasa ta wallafa a X.

Kara karanta wannan

Yadda mutanen kabila baki daya suka musulunta a hannun Sheikh Saidu Jingir

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar da Bola Tinubu ya fitar, ya yi yi ta’aziyya ga daukacin al’ummar Musulmi dangane da wannan babban rashi.

'Sheikh Jingir jagora ne na addini' - Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir a matsayin jagoran addini mai kishin Musulunci.

Ya ce marigayin ya kasance mutum mai kwarewa da ilimi mai zurfi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimin Musulunci da shiryar da al’umma.

Shugaban kasar ya kara da cewa Sheikh Jingir mutum ne da ya samu daukaka a idon jama’a saboda iliminsa da kuma kwarewarsa a tafarkin addini.

Ya ce rasuwar malamin babban rashi ne ga al’ummar Musulmi, domin kuwa ya bar babban gibi a fagen wa’azi da karantarwa.

Tinubu ya ba iyali da almajiran Jingir hakuri

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci iyalan marigayin, abokansa, da almajiransa da su dauki dangana kan rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar malamin Musulunci, Farfesa Pantami ya tura sako ga Yahaya Jingir

Ya ce kowa zai dandana mutuwa kuma babban abin farin ciki shi ne marigayin ya rasu yana kan tafarkin Musulunci, yana hidima ga addini.

Tinubu ya ce ya kamata al’umma su ci gaba da koyon darussa daga irin rayuwar da Sheikh Jingir ya yi, domin yin koyi da irin kyawawan halayensa.

Ya bukaci daukacin al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’a domin Allah Ya gafarta wa marigayin tare da karɓar ayyukansa na alheri.

Marigayi Jingir
Marigayi Sheikh Saidu Jingir. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Asali: Facebook

Tinubu ya roki Allah Ya jikan Sheikh Jingir

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta zunuban Sheikh Saidu Hassan Jingir.

Ya kuma roki Allah Ya ba shi matsuguni mai albarka a Aljannah Firdaus, domin ya kasance cikin wadanda suka rabauta da rahamar Allah.

Tinubu ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’a ga marigayin tare da neman Allah Ya kara wa iyalansa hakuri.

Kara karanta wannan

Yadda rasuwar Sheikh Saidu Jingir ta girgiza gwamnoni da malaman Najeriya

Sheikh Jingir ya musuluntar da kabila

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Saidu Hassan Jingir ya karar da rayuwarsa yana karantar da addinin Musulunci a Najeriya da Afrika.

Legit ta rahoto cewa malamin na cikin malaman da suka yi wa'azi wata kabila baki daya ta Musulunta a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng