Yadda dan sanda ya kashe abokin aikinsa bayan ya sha giya ya yi manƙas

Yadda dan sanda ya kashe abokin aikinsa bayan ya sha giya ya yi manƙas

An kama wani dan sanda mai mukamin saja da ya kashe wani dan sandan mai mukamin sufeta ta hanyar sararsa da adda tare da raunata wani mutum.

A halin yanzu ana tsare da sajan a sashin binciken manyan laifuka (SCIID) da ke Yaba a Legas bayan Sufetan mai suna Francis Adekunle ya mutu a asibiti a ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa sajan ya fita hayyacinsa ne bayan ya dawo daga mashayan giya a kusa da unguwansu da ke Oke-Odo.

Yan sandan biyu suna zaune ne a gidan haya guda tare da wasu yan haya fararen hula. An yi ikirarin cewa wasu yan gidan hayan sun dade suna kuka da halayen sajan.

Dan sanda ya yi makil da giya ya kashe Sifetan Dan sanda
Dan sanda ya yi makil da giya ya kashe Sifetan Dan sanda. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A daren da abin ya faru, an ce sajan ya dawo yana yi wa mutane barazana kamar yadda ya saba idan ya bugu da giya kuma yana bin wani mutum da adda yayin da sufetan dan sandan da ke aiki a Ikeja ya shiga tsakani.

Duk da cewa Sufeta Adekunle yana gaba da shi a wurin aiki, sajan bai yi wata wata ba inda ya juya kansa ya rika sararsa da adda kuma ya yi masa munanan rauni a jikinsa da kafafuwansa.

Rahotanni sun ce an garzaya da shi zuwa asibiti inda ya rasu a ranar Litinin da safe kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wani dan sanda ya ce, "Yana tuka wata mota kirar Toyota Camry mara lamba. An taba kai rahotonsa a caji ofis na Ile Epo da ke Oke-Odo amma ba a dauki wani mataki ba.

"Na ga Sufeta Adekunle a gadon asibiti da dadare. Bai mutu a lokacin. Amma dan uwansa, Ojo Adekunle ya kira ni a waya ya shaida min cewa ya mutu.

"Likita ya tabbatar da mutuwarsa. Ina amfani da wannan dama don kira ga kwamishinan yan sanda CP Hakeem Odumosu ya dauki matakin da ya dace domin gurfanar da wanda ya kashe shi.

"Bai kamata a rika samun irin wannan abin ba a rundunar yan sanda."

Mai magana da yawun yan sandan Legas, Bala Elkana ya tabbatar da kama sajan, ya kara da cewa CP ya bayar da umurnin gudanar da bincike a kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel