Abin Tausayi: Yaran Bello Turji Sun Sace Ɗan Isiyaka Rabiu, Matashin Ya Yi Roko a Bidiyo

Abin Tausayi: Yaran Bello Turji Sun Sace Ɗan Isiyaka Rabiu, Matashin Ya Yi Roko a Bidiyo

  • 'Yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji sun sace wani mutum da ya bayyana kansa a bidiyo a matsayin ɗan Isiyaka Rabiu, yana roƙon a biya kudin fansa
  • Bidiyon da ya bayyana a kafafen sada zumunta ya nuna mutumin cikin damuwa, yana kira ga danginsa su cika sharuddan 'yan bindiga don kubutar da shi
  • Rahotanni sun tabbatar cewa dan bindiga, Turji ya buya bayan farmakin sojoji, inda shi da Dan Isuhu suka tsere, ba tare da bulla a kafafen sada zumunta ba
  • Sojoji sun rusa sansanonin Turji a Shinkafi, tare da cafke mayakansa da dama suka ce za su ci gaba da farmakin har sai sun kawar da 'yan ta'adda

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Wasu gungun 'yan bindiga masu biyayya ga ƙungiyar Bello Turji sun sace wani mutum da ya bayyana kansa cewa shi ɗan Isiyaka Rabiu ne.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, matashin ya roƙi danginsa su biya kuɗin fansa don kubutar da shi ka da yan ta'addan su hallaka shi.

Yaran Bello Turji sun sace wani ɗan Isiyaka Rabi'u a Zamfara
Wani da ke kiran kansa ɗan Isiyaka Rabi'u ya nemi alfarma bayan yaran Bello Turji sun sace shi. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Matashi ya roƙi iyalan Isiyaka Rabi'u alfarma

Rahoton Zagazola Makama ya ce bidiyon da ya bayyana a kafafen sada zumunta ya nuna mutumin cikin firgici da tsoro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon, an gano matashin yana roƙon iyalansa su biya buƙatun waɗanda suka sace shi domin tsira da rayuwarsa.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa sacewar na da alaƙa da saura daga mabiyan Turji, waɗanda farmakin sojoji a Zamfara da makwabtanta ya raunana ƙarfinsu sosai.

A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa Bello Turji ya buya bayan da sojoji suka kai farmaki a sansanoninsa.

Yan bindiga sun sace ɗan Isiyaka Rabi'u
Ana zargin yaran Bello Turji sun sace wani da ya ce shi ɗan Isiyaka Rabi'u. Hoto: @ZagazOlamakama, @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Yadda sojoji suka dagawa Bello Turji hankali

Masu leƙen asiri sun ce Turji da abokinsa, Dan Isuhu, sun sha da kyar a farmakin da ake kai musu wanda a yanzu yan ta'addan ke shan wuta daga rundunar sojoji.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kai hari Borno, sun yi barna kafin isowar sojoji

Sabanin yadda yake alfahari a baya, Turji bai yi magana a kafafen sada zumunta ba, wanda ke nuna yadda farmakin ke masa barazana.

Jami’an tsaro sun rusa wasu sansanonin Turji a Shinkafi da wasu dazuka, tare da cafke mayaka da dama wanda ake zaton na daga cikin dalilin buyan dan ta'addan.

An ce sojoji sun sha alwashin za su ci gaba da farmakin har sai an kawar da 'yan bindiga gaba ɗaya musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Dan bindiga, Abu Radde ya mika wuya

Kun ji cewa ana tsaka da farautar Bello Turji da kara kaimi wurin kakkabe yan ta'adda musamman a shiyyar Arewacin Najeriya, wasu rikakku sun mika wuya.

Rikakken ɗan bindiga, Abu Radde, da yaransa sun miƙa wuya ga jami’an tsaro inda suka saki mutum 10 da suka sace a yarjejeniyar zaman lafiya.

Rahotanni sun ce Abu Radde da wasu ‘yan fashi sun nemi sulhu ta hanyar lumana tare da ganawa da jami’ai a Kwari a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng