Bayan Sauya Shekar El Rufa'i, Tinubu Ya ba Gwamnoni da Ministoci Umarni
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi, ministoci da su kara kokari wajen aiwatar da manufofin da za su amfani talakawa
- Tinubu ya bayyana hakan ne yayin liyafar buda baki da ya shirya tare da gwamnonin jihohi, ministoci da shugabannin hukumomi a Abuja
- Wasu daga cikin manyan jami'an gwamnati sun yaba wa shugaba Tinubu bisa tsare-tsaren da ke rage tsadar rayuwa da inganta tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi, ministoci da su kara zage damtse wajen aiwatar shirye-shiryen da za su amfani talakawa da mabukata.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a daren Litinin yayin da ya karbi bakuncin wasu gwamnonin jihohi, ministoci, da shugabannin hukumomi a liyafar buda baki.

Kara karanta wannan
El Rufa'i na shirin jan 'yan APC zuwa SDP, Tinubu ya yi magana kan tallafin fetur

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Bola Tinubu ya yi ne a cikin wani sako da shafin fadar shugaban kasa ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umarnin Tinubu ga gwamnoni da ministoci
Shugaban kasa Tinubu ya bukaci shugabanni da ke rike da mukaman siyasa da su fifita bukatun talakawa fiye da komai.
Bola Tinubu ya ce:
“Ku ci gaba da kokari, ku kara yin abubuwan da za su amfani mutane.
"Yana da matukar muhimmanci a tabbatar da cewa albarkatun kasa na tafiya ne ga amfanin al’umma ba don wasu kalilan ba.”
Shugaban kasar ya jaddada cewa shugabanci babban nauyi ne da ke bukatar hadin kai da sadaukarwa don tabbatar da jin dadin al’umma.
Tinubu ya kuma bukaci shugabanni da su kasance masu hangen nesa wajen tafiyar da shugabanci domin kafa tarihi mai kyau.
Punch ta ruwaito ya ce:
“Ku dubi kanku a matsayin jagorori da za su kai Najeriya tudun-mun-tsira. Matsayin da na ke kai a yau matsayi ne mai daraja, kuma ba za a yi wasa da shi ba.”

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi abin da ba a yi zato ba kan Osinbajo bayan zaben fitar da gwani a 2023
Martanin gwamnoni ga Bola Tinubu
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yaba wa Tinubu bisa sauye-sauyen tattalin arzikin da ya ke kokarin aiwatarwa.
Gwamnan ya ce:
“Shugaban kasa ya dauki matakai na gaggawa wajen habaka tattalin arziki, kuma muna godiya ga jajircewarsa wajen ganin al’umma sun samu sauki.”
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya ce wannan lokaci ne da ya dace shugabanni su kara hadin kai ba tare da la’akari da banbancin addini ko kabila ba.
Gwamnan ya ce:
“A yanzu haka Musulmai da Kiristoci ke yin azumi a lokaci guda. Wannan yana nuni da cewa Najeriya kasa daya ce da dole ne mu zauna cikin hadin kai.”

Asali: Twitter
Ministoci sun jinjinawa gwamnatin Tinubu
Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya ce ana samun raguwar tsadar kayan masarufi a kasuwanni saboda sauye-sauyen tattalin arziki da ake aiwatarwa.
Fagbemi ya ce:
“Mun lura da cewa ana samun sassaucin farashin kayayyaki a kasuwanni, wanda ke nuna cewa matakan da ake dauka na sauya fasalin tattalin arziki na haifar da da mai ido.”
Fagbemi ya kuma bayyana cewa irin wadannan sauye-sauye suna taimakawa wajen kyautata rayuwar al'umma, tare da jinjina wa shugaban kasa bisa jarumtar sa.
2027: An fara yi wa Tinubu kamfen
A wani rahoton, kun ji cewa jiga jigan jam'iyyar APC sun fara yi wa Bola Tinubu kamfen a jihohin Arewa tun kafin lokacin zabe ya karaso.
Manyan APC kamar Abdullahi Ganduje da gwamnoni da sakataren gwamnatin tarayya sun bukaci al'umma su ba Tinubu dama karo na biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng