Malaman Addini Sun Haɗa Kai, Sun Tunkari Bola Tinubu kan Tsadar Rayuwa

Malaman Addini Sun Haɗa Kai, Sun Tunkari Bola Tinubu kan Tsadar Rayuwa

  • Kungiyar limaman cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) ta nuna damuwa kan tabarbarewar matsalar tattalin arziki da rashin tsaro a kasar nan
  • A taron su na farko na shekarar 2025 a Abuja, limaman cocin sun bukaci gwamnati da ta canja salonta don shawo kan wadannan matsalolin
  • Shugaban CBCN, Archbishop Lucius Ugorji, ya jaddada cewa talauci ya yi kamari, inda kimanin mutane miliyan 129 ke cikin mawuyacin hali

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar limaman Katolika ta Najeriya (CBCN) ta yi gargadi cewa wahalar tattalin arziki, rashin tsaro da rashin aikin yi ga matasa sun tabarbare matuka.

A yayin taronsu na farko na 2025 a Abuja, CBCN ta bukaci gwamnati gaggauta daukar matakin magance hauhawar farashin abinci da garkuwa da mutane.

Kungiyar CBCN ta malaman cocin Katolika sun yi magana da tattalin arziki da tsaro a Najeriya
Malaman cocin Katolika sun nuna damuwa akan tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro. Hoto: @Sanothomas
Asali: Twitter

Malaman cocin Katolika sun magantu kan tattali

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya samu halartar shugabannin addini, ciki har da Archbishop Lucius Ugorji, shugaban CBCN, da Archbishop Daniel Okoh, shugaban CAN, inji rahoton Vanguard.

Malaman cocin Katolikan su bukaci gwamnati ta magance tushen matsalar tattalin arziki da tsaro, tare da jaddada cewa ‘yan Najeriya na fama da matsanancin fatara.

Archbishop Ugorji ya yabawa gwamnati kan ɓullo da shirin ba dalibai rance, gyaran hanyoyi da sauransu, amma ya ce shirye-shiryen ba su wadatar ba.

Ana so gwamnati ta canja salon yaki da talauci

Ya bayyana cewa duk da matakan gwamnati, hauhawar farashi na ci gaba karuwa, kuma rayuwa ta kara tsada, inda yawancin ‘yan kasa ke cikin matsananciyar wahala.

"A halin yanzu, hauhawar farashin abinci ya kai kashi 39.84%, wanda ke hana iyalai samun damar cin abinci sau uku a rana," inji Ugorji.

Ya kara da cewa akwai bukatar gwamnati ta canja salo kan magance talauci bayan alkaluma sun nuna cewa mutum miliyan 129 na fama da matsanancin talauci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan an yi garkuwa da shi, wani babban malamin addini ya rasu a Kaduna

Malaman Katolikan sun jaddada cewa tallafin abinci da gwamnati ke bayarwa ya yi kadan, yana mai cewa ana bukatar matakan da za su magance matsalar na dogon lokaci.

Malaman Kotolika sun koka kan matsalar tsaro

Kungiyar malaman cocin Katolika sun nuna damuwa kan matsalar tsaro a Najeriya
Malaman cocin Katolika sun nemi gwamnati ta canja salo wajen yaki da talauci da matsalar tsaro. Hoto: @Sanothomas
Asali: Twitter

Sun kuma nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro, inda hare-haren ‘yan Boko Haram, ‘yan bindiga da wasu ‘yan tada kayar baya ke karuwa.

Jagororin cocin sun ce matsalar garkuwa da mutane ta kara muni, inda shugabannin addini suka zama sababbin wadanda ake yin garkuwa da su.

The Nation ta rahoto Ugorgi ya buga misali da sace Fr. Philip Ekweli da wani dalibin firistanci, da kuma kashe Fr. Sylvester Okechukwu a matsayin illar rashin tsaro a kasar.

"Kasar nan na fuskantar barazana. Kowacce rana, ana jin labarin sace mutane da kisa ba tare da hukumomi sun dauki mataki ba.
"Hatta malaman addini ba a kyale su ba. Har yaushe za mu ci gaba da rayuwa a cikin tsoro?"

Kara karanta wannan

"Ku bi a hankali," Omokri ya bukaci CAN ta guji shari’a da jihohi kan hutun Ramadan

- Archbishop Lucius Ugorji

Sun bukaci gwamnati da ta kara kaimi wajen yaki da ‘yan ta’adda, ta bunkasa tattara bayanan sirri da samar da kayan aiki ga jami’an tsaro.

CBCN ta gargadi Tinubu kan cire tallafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar malaman cocin Katolika (CBCN) ta nuna damuwa kan cire tallafin mai, tana mai cewa lamarin na barazana ga kasa.

CBCN ta jaddada cewa rashin ingantattun tsare-tsare na rage radadin cire tallafin na haifar da matsaloli masu tsanani ga tattalin arzikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.