Gwamnatin Tinubu Ta Tsoma Baki kan Zargin Shugaban Majalisa da Neman Matar Aure

Gwamnatin Tinubu Ta Tsoma Baki kan Zargin Shugaban Majalisa da Neman Matar Aure

  • Gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar harkokin mata za ta shiga tsakani da nufin sasanta rigimar shugaban majalisar dattawa da Sanatar Kogi
  • Ministar harkokin mata a Naje, Imaan Suleiman Ibrahim ta ce za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen sasanta rikicin da ta kira da babban abin takaici
  • Ta kuma buƙaci shugabanni siyasa da su gujewa ɗaukar matakan da za su rage wa mata ƙwarin guiwar shigowa a dama da su a harkokin mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta shiga tsakani domin warware rikicin da ke faruwa a Majalisar Dattawa.

Ministar harkokin mata, Imaan Suleiman Ibrahim, ta yi alkawarin shiga tsakani domin sasanta rikicin da ke tsakanin Godswill Akpabio, da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Ministar mata, Imaan Suleiman Ibrahim.
Gwamnatin Tinubu za ta shiga tsakani domin sasanta Akpabio da Natasha Hoto: @hm_womenaffairs
Asali: Twitter

Majalisa ta dakatar da Sanata Natasha

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa a ranar Alhamis, Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha daga Kogi na tsawon watanni shida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin ladabtarwa da ɗa'a na Majalisa ya bayyana cewa Sanatar ta saba ka’idojin majalisa, shiyasa aka dakatar da ita.

Da take jawabi ga ’yan jarida bayan wani taron manema labarai da aka shirya domin bikin Ranar Mata ta Duniya (IWD), Ministar ta bayyana matakin da aka dauka a matsayin abin takaici.

Gwamnatin Tinubu ta nemi a sasanta

Imaan Suleiman ta kuma yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su nemi hanyar da za a kawo karshen rikicin cikin lalama.

“Wannan wani lamari ne mai ban takaici da bai kamata ya faru ba. Kamar yadda kuka ambata, a majalisa ta baya muna da mata sanata guda tara.
A wannan majalisa, muna da guda hudu kacal. Ba ma son rasa kowace memba a Majalisar Dattawa ko Majalisar Wakilai, sai dai ma kara adadinsu.”

Kara karanta wannan

Sanatan Katsina ya fusata, ya soki sharadin yi wa Natasha afuwa

Ministar ta jaddada cewa mata na bukatar karin wakilci a manyan mukaman siyasa, domin su samu damar kare muradun mata da kananan yara a kasar nan.

Natasha: Ministar mata ta nuna damuwa

Ta bayyana damuwarta cewa dakatar da Sanata Natasha zai rage tasirin mata a majalisa, wanda ke da illa ga burin samun daidaito tsakanin maza da mata a siyasa.

“Lamarin abin takaici ne, amma za mu shiga tsakani don sasanta rikicin. Za mu tattauna da dukkan bangarorin da abin ya shafa domin a yi adalci cikin tausayi.
"Na je Majalisar jiya, inda aka gudanar da bikin Ranar Mata ta Duniya, kuma kalmar karshe da Shugaban Majalisar Dattawa ya fada ita ce ‘muna da niyyar sasantawa.’”
Natasha da Akpabio.
Ministar mata ta buƙaci shugabanni su daina ɗaukar matakan da za su cire wa mata sha'awar shiga harkokin mulki Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Ta kara da cewa,

Za mu kasance masu shiga tsakanin wadannan bangarorin guda biyu domin samar da zaman lafiya.
"Haka nan, za mu ci gaba da wayar da kan jama’a domin ganin cewa mata da maza sun fi yin aiki tare cikin fahimta da jituwa.”

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha ta sake yamutsa Hazo, ta yi magana kan dakatar da ita

A karshe, Ministar ta bukaci a yi adalci ga kowa, tare da yin kira ga shugabannin siyasa da su daina daukar matakan da za su rage karfin wakilcin mata a gwamnati.

Sanata Natasha ta yi fatali da dakatarwa

A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce matakin da majalisa ta ɗauka a kanta babu adalci a ciki.

Sai dai sanatar ta bayyana cewa za ta ci gaba da yi wa al'ummar da suka zaɓe ta hidima kuma dakatarwar da aka mata ba bisa ƙa'ida ba, ba za ta hana ta aiki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262