Bidiyo: Zanga Zanga Ta Barke bayan Shiga Asibiti a Kama Dan Najeriya a Amurka

Bidiyo: Zanga Zanga Ta Barke bayan Shiga Asibiti a Kama Dan Najeriya a Amurka

  • Jami'an ma'aikatar shige da fice ta Amurka sun kama wani dan Najeriya a cikin wani asibiti, lamarin da ya dauki hankalin al'umma da dama
  • Kama mutumin duk da cewa yana asibiti ne ya tayar da zanga-zanga mai muni a New York, lamarin da ya jawo kama mutane da yawa a yankin
  • Hukumomin kasar Amurka sun bayyana dalilan kama dan Najeriyan tare da fadin laifin da ake zargi ya aikata a zaman da ya yi a birnin New York

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta ce ta kama wani dan Najeriya mai suna Chidozie Wilson Okeke bisa zargin aikata laifuffuka da suka hada da mallakar miyagun kwayoyi ba bisa ka’ida ba.

A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga jami’an hukumar kula da shige da fice (ICE) suna jan Okeke a kasa, an sa masa ankwa, bayan sun fitar da shi daga asibiti suka saka shi a cikin motarsu.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Jami'an Amurka na neman kama wani matashi
Yadda jami'an Amurka suka nufi cafke wani matashi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da BBC ta wallafa ya nuna cewa lamarin ya faru ne a asibitin Wyckoff Heights da ke birnin New York a daren ranar Asabar.

An yi zanga-zanga a kasar Amurka

A daren Asabar din, an yi zanga-zanga a gaban asibitin saboda kama Okeke da jami’an ICE suka yi, lamarin da ya kai ga cafke wasu daga cikin masu adawa da matakin.

Mutane da dama sun taru a gaban asibitin suna zanga-zanga kan yadda ICE ke korar baki da yawa karkashin gwamnatin Shugaba Donald Trump.

Ga bidiyon da Al Jazeera ta wallafa a X game da lamarin:

Dalilan kama dan Najeriya a Amurka

Sai dai a ranar Litinin, ICE ta ce an kama Okeke ne saboda zargin mallakar miyagun kwayoyi da kuma wuce wa’adin bizar da ya yi tun 2023.

A wata sanarwa da ICE ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa bayan wani shiri na musamman da suka gudanar a Brooklyn, sun kama Okeke bisa zargin aikata laifukan mallakar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

White House: An shiga fargaba bayan harbi a kusa da fadar shugaba Trump

Hukumar ta ce yayin da suke kokarin kama shi, Okeke ya ki bin umarnin jami’ai, har ma ya yi kokarin kai musu hari, amma jami’an sun yi amfani da karfi domin kama shi.

“Yayin kama shi, Okeke ya ki bin umarnin jami’ai na fita daga mota kuma ya yi kokarin amfani da motar wajen bugun jami’an ICE.
“Ya kuma yi yunkurin duka da kai musu mari, amma jami’anmu sun bi ka’idoji tare da amfani da karfi kadan da ya dace wajen kama shi,”

In ji sanarwar.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka na jawabi a wajen wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

An yi harbi a fadar Shugaban Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa jami'an leken asirin Amurka sun yi karin bayani game da wani harbi da aka yi a kusa da fadar White House.

Hukumar leken asirin kasar ta sanar da cewa ta kama wani mutum da ya budewa jami'anta wuta a lokacin da suka yi yunkurin bincikensa.

An bayyana cewa an harbi mutumin yayin da ya ciro bindigar shi, sai dai hukumomin Amurka sun ce bai mutu ba, yana karbar magani a asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng