Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara, Sun Hallaka Manyan Kwamandojin Boko Haram

Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara, Sun Hallaka Manyan Kwamandojin Boko Haram

  • Dakarun sojojin Najeriya sun ragargaji ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram a wani artabu da suka yi a jihar Borno
  • Sojojin sun farmaki ƴan ta'addan a maɓoyarsu bayan sun samu bayanan sirri kan motsinsu a ƙaramar hukumar Bama
  • A yayin artabun, sojojin sun hallaka ƴan ta'addan Boko Haram tara, ciki har da babban mai haɗa bama-bamai ga ƙungiyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun hallaka aƙalla ƴan ta'adda Boko Haram guda tara a jihar Borno.

Sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne ciki har da Amirul Bumma, babban mai haɗa bama-baman ƙungiyar Boko Haram a wata fafatawa mai zafi a dajin Sambisa.

Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a Borno Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka ragargaji ƴan Boko Haram

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke tsohon jami'in tsaro mai safarar makamai ga 'yan bindiga

Majiyoyi sun bayyana cewa arangamar ta faru ne a ƙaramar hukumar Bama yayin wani samamen ƙaƙƙabe ƴan ta'adda da rundunar Operation Desert Sanity 4 ta kai.

Dakarun sojojin sun kai farmakin ne tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro bayan samun bayanan sirri kan motsin ƴan ta'addan.

Bayanan sun nuna cewa ƴan ta'addan suna taruwa a wani sansani da ke tsakanin Sabil Huda da Njimiya, kusa da Alai Dala.

Ƴan ta’addan waɗanda aka shammata, sun yi ƙoƙarin yin turjiya, amma sojojin sun yi nasarar fatattakar su da ƙarfin wuta.

Bayan yaƙin, an lura cewa ƴan ta’addan sun kawo gadajen asibiti zuwa filin daga, wanda ke nuna irin ɓarnar da aka yi musu.

Bincike ya nuna cewa manyan kwamandojin Boko Haram da aka kashe sun haɗa da, Amirul Bumma, babban mai haɗa bama-bamai na Boko Haram.

Bayan shi kuma akwai irinsu Bakura Ghana, Awari da wani Malam Kalli.

Sauran sun haɗa da Malam Usman Bula Kagoye, Ibrahim Bula Abu Asma’u, da wasu mutum biyu da ba a tantance sunayensu ba tukuna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a kauyen Katsina duk da sulhun da aka yi da su

Baya ga hallaka waɗannan ƴan ta’addan, sojojin sun ƙwato makaman yaƙi masu yawan gaske.

Sojoji sun daƙile mugun nufin Boko Haram

Hakazalika a ƙoƙarinsu na ɗaukar fansa, mayakan na Boko Haram sun dasa abubuwa masu fashewa da yawa a hanyar da sojojin za su wuce.

Duk da haka, sojojin sun gano mugun nufin na su, kuma sun tarwatsa kusan guda 10 daga cikinsu, wanda hakan ya hana a samu asarar rayuka.

Babban kwamandan runduna ta bakwai, Manjo Janar Abubakar Haruna, ya yaba da nasarar da sojojin suka samu kan ƴan ta'addan.

Ya jinjinawa jarumtarsu tare da jaddada ƙudirin rundunar sojojin wajen kawar da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da kuma faɗin Najeriya.

Ƴan Boko Haram sun kai hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a jihar Borno da aka dade ana fama da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno, sun sace babban farfesa da fasinjoji

Ƴan ta'addan waɗanda suka kai harin a ƙauyen Kaleri da ke ƙaramar hukumar Mafa, sun sace mutum biyu tare da kwashe dukiya mai tarin yawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng