Sojoji Sun Lakadawa Ma'aikatan Lantarki Duka bayan Yanke Wuta a Bariq2ki

Sojoji Sun Lakadawa Ma'aikatan Lantarki Duka bayan Yanke Wuta a Bariq2ki

  • Rahotanni na nuni da cewa wasu sojoji sun afka hedikwatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja da ke Legas
  • Ana zargin cewa cewa sojojin sun ci zarafin ma’aikata, inda aka ga wasu na kwance suna karbar duka a cikin ofishin
  • Lamarin ya samo asali ne bayan kamfanin rarraba wutar ya katse lantarki a sansanin sojin saman Najeriya a Ikeja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - An samu rahotanni cewa wasu sojoji dauke da makamai sun afka ofishin kamfanin rarraba wuta na Ikeja da ke gabanin MITV a jihar Lagos.

A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:40 na safiyar Alhamis inda aka ga sojojin na cin zarafin ma’aikatan kamfanin.

Kara karanta wannan

Duk da korafin CAN a jihohi, an fara hutun azumin Ramadan a jami'ar tarayya

Legas
Sojoji sun lakadawa ma'aikatan lantarki wuta. Hoto: @NigeriaStories
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa sojojin sun lakadawa wasu daga cikin jami'an kamfani duka bayan isarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun yi wa ma'aikatan lantarki duka

Wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda sojojin ke dukan ma’aikatan, wasu na durkushe a kasa suna karbar horo.

The Cable ta wallafa cewa irin wannan farmakin ya faru a wani ofishin rarraba wuta na Ikeja da ke Ago Palace Way, Okota, Isolo.

Dalilin rikicin tsakanin sojoji da kamfanin wuta

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa kamfanin rarraba wutar ya katse wutar sansanin sojin saman Najeriya da ke Ikeja a ranar Laraba.

An ruwaito cewa sansanin sojojin ya shafe makonni biyu babu wuta sakamakon rashin biyan bashin da ake bin su da ya kai miliyoyin Naira.

Kamfanin Ikeja Electric ya tsorata da lamarin

Wani ma’aikacin kamfanin Ikeja Electric ya bayyana cewa har yanzu ba su san inda wasu daga cikin abokan aikinsu suke ba tun bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga ya tono sirrin 'yan ta'adda ga sojoji kafin 'yan uwasa su harbe shi

Ma'aikacin ya ce:

“Mun kasa samun shugabanninmu a waya, babu tabbas ko an ci zarafinsu ko kuma sun buya don tsira da rayukansu.”
sojoji
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Musa. Hoto: Defence Headquarters
Asali: Facebook

Me ya fusata sojojin kan wutar lantarki?

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa akwai yarjejeniya da ke tsakanin Ikeja Electric da sojojin saman Najeriya.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa dole sojojin su biya ₦60m duk wata domin samun wuta na awanni 10 zuwa 12 a kowacce rana.

Rahotanni sun tabbatar da cewa rashin wuta a sansanin sojojin yana barazana ga tsaron sansanin, musamman duba da cewa akwai wuraren ajiyar makamai masu hadari a ciki.

Kamfanin wuta ya dage sai an biya bashi

Wasu majiyoyi daga kamfanin Ikeja Electric sun ce sojojin ba su cika alkawarin biyan kudin wutar ba, lamarin da ya sa suka dauki matakin yanke musu wuta.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ofisoshin Ikeja Electric ba su koma bakin aiki ba saboda tsoron farmakin sojojin.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

NLC za ta yi zanga zanga kan lantarki

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin kwadago sun yi barazanar shirya gagarumar zanga zanga a dukkan jihohin Najeriya kan karin kudin wuta.

'Yan kwadago sun yi gargadin ne biyo bayan wani jawabi da ministan makamashin Najeriya ya yi na cewa 'yan Najeriya su shirya karin kudin wuta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng