Katsina Ta Cika da Baki da Aka Nada wa ’Dan Gwamna Dikko Radda Sarauta a Jihar
- Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, ya jagoranci nadin sarautar dan Gwamna Dikko Umaru Radda a jihar
- Taron naɗin sarautun ya samu halartar gwamnoni, sarakuna da manyan baƙi daga sassan Najeriya da kuma jamhuriyar Nijar makwabciya
- Sarkin Katsina ya yi kira ga jama’a su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da kyawawan ɗabi’u domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a al’umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, ya jagoranci babban bikin naɗin sarauta na sababbin hakimai uku a fadar masarautar Katsina.
Daga cikin waɗanda aka naɗa har da Alhaji Muhammadu Dikko Radda, ɗan Gwamna Dikko Umaru Radda, wanda aka ba sarautar Gwagwaren Katsina II da Hakimin Radda.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar a shafinta na X a yau Asabar 1 ga watan Mayun 2026.
Sauran wadanda suka samu sarauta a Katsina
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Ahmad Abdulmumini Kabir Usman wanda ya zama Danmajen Katsina da Hakimin Dankama.
Haka kuma an naɗa Alhaji Abubakar Dardisu a matsayin Sarkin Mudurun Katsina tare da ba shi sarautar Hakimin Muduru a jihar Katsina.
Bikin ya samu halartar manyan baƙi daga sassan Najeriya da maƙwabciyar jamhuriyar Nijar tare da godiya ga Sarkin Katsina bisa wannan nadin sarauta da ya yi.
Gwamna Radda ya karbi bakuncin Abba Kabir
Majiyoyi suka ce manyan mutane a fadin Najeriya cikin har gwamnoni da sarakunan gargajiya da yan siyasa yan kasuwa da sauran fitattun mutane a ciki da wajen Katsina sun shaida nadin sarautar.
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, da takwaransa na Kano, Abba Kabir Yusuf, da Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto sun halarci bikin tare da sauran jami’an gwamnati inda aka cika wurin taron babu masaka tsinke.
Har ila yau, shugaban majalisar dokokin Katsina, Nasir Yahaya Daura, da wasu fitattun mutane sun kasance cikin mahalarta taron naɗin sarautun.

Kara karanta wannan
Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

Source: Facebook
Jawabin kan hankali daga Sarkin Katsina ga al'umma
A jawabin da ya gabatar, Sarkin Katsina ya bayyana bikin a matsayin mafi girman taron da aka taɓa yi a zamanin mulkinsa.
Sarkin ya yaba wa mahalarta bisa nuna ladabi da haɗin kai, sannan ya buƙaci jama’a su rungumi zaman lafiya da mutunta juna a ko da yaushe.
Ya kuma gargadi jama’a kan hassada da rashin haɗin kai, yana mai cewa addini da tarbiyya na da muhimmanci wajen gina al’umma mai ci gaba.
Radda ya kaddamar da Majalisar sarakuna
An ji cewa Gwamna Dikko Umaru Radda ya kaddamar da majalisar masarautun jihar Katsina don karfafa dangantakar gwamnati da sarakuna.
Sarkin Katsina ya zama shugaban majalisar, yayin da sarkin Daura ke matsayin mataimaki, tare da wakilan addini, 'yan kasuwa da matasa.
Majalisar za ta ba da shawarwari kan shari’a, al’adu, tsaro, zaman lafiya, raya al’umma da kare muhalli a Katsina, a cewar Dikko Radda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
