"A Yi wa Musulmai Adalci," MURIC Ta Yi Kaca Kaca da Gwamnatin Tinubu kan Fifita Kiritoci

"A Yi wa Musulmai Adalci," MURIC Ta Yi Kaca Kaca da Gwamnatin Tinubu kan Fifita Kiritoci

  • Kungiyar MURIC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da fifita kiristoci sama da musulmi a wasu ayyukanta
  • Shugaban MURIC na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ya ce dole gwamnatin tarayya ta yi adalci da daidaito a dukkan al'amurranta
  • Akintola ya bayyana aikin gina coci da cibiyar hajjin kiristoci da za a gina a Abuja kan N25bn a matsayin misalin banbancin da ake nuna wa Musulmi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja – Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta zargi gwamnatin tarayya da nuna wariya kan aikin gina coci da cibiyar hajjin Kirista da kudinsu ya kai Naira biliyan 25.

Za a gina wannan babbar coci da cibiyar ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya Abuja.

Akintola.
Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: MURIC, @aonanuga1956
Source: Facebook

Daily Trust ta ce a wata sanarwa da shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar, ya kuma soki gwamnatin kan bayar da Naira biliyan 2 ga wadanda rikici ya shafa a jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Abba ya kinkimo aiki, za a kashe sama da N21bn don jiƙa Kanawa da ruwan sha

MURIC ta taso Gwamnatin Bola Tinubu

Akintola ya soki tallafin da aka ba wadanda rikici ya shafa a jihar Filato ba tare da ba da irin wannan tallafi ga jihohin Borno, Sokoto, Zamfara, Kebbi da Kwara ba.

“Gwamnatin tarayya da kungiyar CAN sun kaddamar da gina wata babbar coci da cibiyar hajji a filin jirgin sama na Abuja da kudinsu ya kai Naira biliyan 25.
“Ya kamata gwamnati ta bayyana dalilin wannan fifiko take nuna wa kiristoci. Musulman Najeriya sun cancanci a yi musu adalci.
"Ana ta ce-ce-ku-ce a masallatai da kafafen sada zumunta na Musulmi kan wannan lamari.”

- Farfesa Ishaq Akintola.

Kungiyar MURIC ta fadi dalilanta

Akintola ya kuma bayyana damuwa kan yadda aka bai wa jihar Plateau Naira biliyan 2, yayin da sauran jihohin da ke fama da irin wannan rikici ba su samu irin wannan tallafi ba.

Ya tambaya ko wannan adalci ne, yana mai cewa bai dace a nuna bambanci tsakanin al’umma ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta amince da bukatar gwamnatin Tinubu a shari'ar mutane 6 da ake zargi da shirin juyin mulki

Ya kuma ambaci wani zargin bayar da Naira biliyan 1.2 ga jihohi 19 na Arewa domin bikin Sallah, yana mai cewa ba a bayyana wanda ya bayar da kudin ba.

“Ta yaya za a bai wa jiha guda Naira biliyan 2, sannan a raba 'Naira biliyan 1.2 ga jihohi 19? Shin hakan daidai ne?”
Farfesa Akintola.
Shugaban kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC a Najeriya, Farfesa Ishaq Akintola Hoto: @Instablog
Source: Twitter

Shawarar da MURIC ta ba gwamnati

Kungiyar MURIC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta bayyana lokacin da za ta bai wa Musulmi fili makamancin wannan domin gina babban masallacin kasa, tare da irin tallafin da aka bayar wajen aikin cocin.

Ta jaddada cewa dole ne a yi adalci da daidaito tsakanin Musulmi da Kiristoci a dukkan lamurra na gwamnati, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ana zargin ba a yi wa musulmi adalci a Jos

A wani labarin, kun ji cewa wani malamin Musulunci, Imam Tajuddeen Muhammad Adigun, ya yi kakkausar suka kan yadda ake dorawa musulmi laifi a rikicin jihar Plateau.

Malamin ya ce Musulmi ma suna fuskantar hare-hare da kashe-kashe ba tare da samun adalci ba kamar yadda aka yi a baya.

Malamin ya jaddada cewa Musulunci ba ya goyon bayan kashe-kashe ko zalunci, yana mai cewa addinin ya haramta kisan bayin Allah marasa laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262