An Sha Mamaki da EFCC ta Yi Wa'azi da Kur'ani kan Rashawa a Najeriya

An Sha Mamaki da EFCC ta Yi Wa'azi da Kur'ani kan Rashawa a Najeriya

  • EFCC ta yi amfani da darajar Juma’a a cikin watan Ramadan domin jaddada aikinta na yaki da cin hanci da rashawa
  • Hukumar ta ambaci wata aya daga Alkur’ani mai girma domin yin kashedi ga mutane kan wawure dukiyar da ba ta su ba
  • Al’ummar Najeriya sun yi mamakin wannan sabon salo da EFCC ta dauka wajen fadakarwa a game da cin amanar dukiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya (EFCC) ta yi amfani da muhimmancin Juma’a a watan Ramadan domin jaddada aikinta na yaki da cin hanci.

A cikin wata fadakarwa da ta janyo ce-ce-ku-ce, hukumar ta ambaci wata aya daga Alkur’ani domin yin gargadi kan wawure dukiyar al’umma da kuma dabi’ar almundahana a harkar kudi.

Kara karanta wannan

Amurka ta sake tsoma baki kan tsaron Najeriya, ta yi korafi kan kashe kashe

Hukumar EFCC
EFCC ta yi wa'azi da kur'ani. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Legit Hausa ta tattaro cewa hukumar EFCC ta yi nasihar ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar EFCC ta yi wa’azi da aya daga Alkur’ani

A cikin wani sako da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, EFCC ta ambaci aya ta 29 a suratul Nisa’i, wacce ta ce:

"Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku ci dukiyoyinku da zalunci, sai dai ta hanyar kasuwanci da akwai yarda da juna..."

Hukumar ta sanya sakon tare da hoto mai dauke da wata hannu da ke fizgar kudi, tare da bude Alkur’ani a kusa da shi, domin nuna nauyin da ke tattare da amana da gaskiya a harkar kudi.

EFCC ta yi amfani da ranar Juma’a a Ramadan

Zabin yin wannan wa’azi a ranar Juma’a cikin watan Ramadan na da nufin jaddada muhimmancin kauce wa rashawa da zalunci a wannan wata mai tsarki.

Kara karanta wannan

Tsohuwar ministar Tinubu ta kwana a hannun EFCC kan zargin karkatar da N138m

A cikin wannan wata, Musulmai sukan maida hankali wajen takaita kansu, yin tunani da kuma tsarkake halayensu.

Yin amfani da aya daga Alkur’ani domin fadakar da al’umma kan haramcin rashawa na nuna cewa cin hanci ba wai laifi ne kawai a idon doka ba, har ma da zunubi ne a addini.

EFCCN
Shugaban hukumar EFCC a wani taro. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Martanin 'yan Najeriya kan wa'azin EFCC

Wasu daga cikin ‘yan Najeriya sun jinjinawa EFCC kan amfani da bangaren addini domin fadakarwa kan rashawa.

Sabanin haka, wasu kuma sun nuna shakku kan ko hakan zai haifar da sakamako mai kyau a tsakanin mutane.

Wasu kuma sun bayyana cewa irin wannan wa’azi ya kamata ya shafi addinai daban-daban domin tabbatar da adalci ga kowa.

Ga wasu daga cikin martanin da Legit.ng ta tattara daga jama’a a kafar X:

@NazifMusah ya yi martani da cewa:

"Ina farin ciki da irin yadda kuke hulda da jama’a. Tare za mu yaki cin hanci da rashawa in shaa Allah."

Kara karanta wannan

Kwamishinonin El Rufa’i sun bayyana gaskiyarsu kan zargin karkatar da N1.37bn

Sai da kuma @DanielIfec99309 ya nuna shakku inda ya ce:

"Ba ku yin aikinku yadda ya kamata."

@BuraimohAbiodun ya yi tambaya da cewa:

"Ko dai kuna nuna son kai a yaki da rashawa ko kuma ba ku da karfin fada a ji. Me kuke yi kan ‘yan siyasar da ke da shari’a a kotu?"

@chukwud83598022 ya yi martani da cewa:

"Kun san dai babu wata doka da ta ba ku ikon yin wa’azi, ko?"

EFCC ta kama tsohuwar ministar mata

A wani rahoton, kun ji cewa hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta kama tsohuwar ministar mata.

An kama tsohuwar ministar matan da shugaba Bola Tinubu ya sauke a 2024 ne kan zargin karkatar da wasu makudan kudi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng