Amurka Ta Sake Tsoma Baki kan Tsaron Najeriya, Ta Yi Korafi kan Kashe Kashe
- Amurka ta yi Allah wadai da kisan wani malamin Kirista, Rabaran Sylvester Okechukwu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a Kaduna
- Rabaran Okechukwu ya shiga hannun masu garkuwa da mutane a ranar 4 ga Maris, 2025, kuma an kashe shi washe gari a ranar Laraba
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tura jami’anta domin kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki, aka yi kira da a tabbatar da adalci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bayyana matukar damuwa da takaici kan kisan Rabaran Sylvester Okechukwu.
'Yan bindiga ne suka yi garkuwa da Faston, suka kuma kashe shi a wani yanki na jihar Kaduna a makon da ya wuce.

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

Asali: Facebook
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, ofishin kasar Amurka a Najerya ta bayyana kisan a matsayin mugun aiki da rashin imani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bukaci hukumomi da su tabbatar da ganin an hukunta wadanda suka aikata kisan malamin addini ba tare da wata-wata ba.
Sanarwar ta ce:
“Ofishin akadancin Amurka ya cika da bakin ciki da takaici kan kisan Rabaran Sylvester Okechukwu a jihar Kaduna, Najeriya.
"Mun yi Allah wadai da wannan mugun aiki na rashin imani. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalai, mabiyan cocin Rabaran Okechukwu, wadanda suka rasa masoyinsu.
"Muna tare da su a wannan lokaci na alhini. Muna kira ga hukumomi da su tabbatar da ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.”
Yadda aka kashe Faston a Kaduna
Malamin cocin Katolika da ke Tachira, Karamar Hukumar Kaura, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane ne daga gidansa a daren Talata, 4 ga Maris, 2025.
A cewar sakataren cocin Katolika na Kafanchan, Jacob Shanet, an kashe shi a safiyar Laraba, 5 ga Maris, ranar wani taro mai muhimmanci a kalandar Kiristoci.
Shanet ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa:
“Bayan an yi garkuwa da shi, muna mai bakin cikin sanar da ku cewa an kashe Rabaran Sylvester da safiyar yau, 5 ga Maris, 2025.
"Har yanzu ba a san dalilin da yasa aka kashe shi ba.”
An taba yunkurin sace Faston a baya
Legit ta rahoto cewa an haifi Rabaran Okechukwu a ranar 11 ga Disamba, 1980, kuma an naɗa shi malamin Katolika a ranar 11 ga Fabrairu, 2021.
Wannan ba shi ne karon farko da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi ba; a watan Disamba na 2022, an taba yin garkuwa da shi daga wani coci da ke Fadan Kono, Karamar Hukumar Kauru.
Bayan shafe kwana uku a hannun masu garkuwa, an sake shi, amma a wannan karon, sakamakon lamarin bai yi kyau ba.

Asali: Facebook
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar lamarin, kakakinta, Mansir Hassan, ya ce jami’anta sun bazama domin kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.
An kashe masu garkuwa a jihar Delta
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen gari sun hadu sun tunkari 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Delta.
Biyo bayan lamarin, mutanen garin sun kashe masu garkuwa guda uku bayan an musu dukan kawo wuka tare da kubutar da wadanda suka sace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng