Tsohuwar Ministar Tinubu Ta Kwana a Hannun EFCC kan Zargin Karkatar da N138m

Tsohuwar Ministar Tinubu Ta Kwana a Hannun EFCC kan Zargin Karkatar da N138m

  • Tsohuwar Minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara amsa tambayoyi a kan zargin badakalar karkatar da kudi a lokacinta
  • Uju Kennedy Ohanenye ta kwana a hannun jami’an EFCC bayan zargin karkatar da kudin da aka ware wa ma’aikatar Harkokin Mata
  • Hukumar EFCC ta ce bincikenta ya gano cewa wasu kudin shirin tallafawa mata an karkatar da su ba bisa ka’ida ba
  • Ana zargin badakalolin tsohuwar Ministar na cikin dalilan da ya jawo mata asarar kujerarta a lokacin da Tinubu ya yi garanbawul

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaTsohuwar Ministar Mata, Uju Kennedy Ohanenye, ta kwana a karon farko a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) bayan da jami’an hukumar suka tsare ta ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kwamishinonin El Rufa’i sun bayyana gaskiyarsu kan zargin karkatar da N1.37bn

Jami’an EFCC sun yi mata tambayoyi kan zargin karkatar da kudie da saba ka’idojin sayo kayan gwamnati a ma’aikatar da ta shugabanta a lokacin mulkinta.

Uju kennedy
Tsohuwar Minista ta kwana a hannun EFCC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Uju Kennedy Ohanenye
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta wallafa cewa tsohuwar ministar na fuskantar zargin karkatar da N138,413,253.89, kudin da aka ware a kasafin kudin shekarar 2023 don ayyukan ma’aikatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta zargi tsohuwar Minista da almundaha

Wata majiya daga EFCC ta ce Ohanenye ta isa shelkwatar hukumar a ranar Alhamis da misalin karfe 11:00 na safe, inda aka fara yi mata tambayoyi dangane da zargin da ake yi mata.

Kennedy
Tsohuwar Ministar ta fada komar EFCC Hoto: Uju Kennedy Ohanenye
Asali: Facebook

Majiyar ta bayyana cewa binciken da EFCC ta gudanar ya gano cewa kudin da aka bayar don shirin tallafa wa mata na shugaban kasa sun shiga hannun wasu mutane ba bisa ka’ida ba.

Majiyar ta ce:

“Jami’an EFCC na bincikar tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy Ohanenye, dangane da zargin karkatar da kudi wanda ya kai kimanin N138,413,253.89,”

Kara karanta wannan

Wata 5 bayan Tinubu ya kore ta, EFCC ta tsare tsohuwar Minista kan zargin kwashe N138m

“Ta isa shelkwatar hukumar da misalin karfe 11:00 na safe a ranar Alhamis, kuma ana ci gaba da yi mata tambayoyi kan rawar da ta taka a cikin wannan badakala.”

- inji majiyar

Tinubu ya sauke Uju daga mukamin Minista

Uju Kennedy Ohanenye na daga cikin ministocin da aka sauke daga mukamansu bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya karo na 19 da aka gudanar a fadar shugaban kasa a watan Oktoba 2024.

Bayan sauke ta, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbinta da tsohuwar Ministar Harkokin ‘Yan Sanda, Imaan Suleiman-Ibrahim domin a ci gaba da kula da harkokin ma'aikatar.

EFCC ta fara binciken tsohuwar Ministar mata

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawatana gudanar da bincike kan tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, kan zargin karkatar da N138m.

Wani jami’in EFCC ya bayyana cewa an tsare tsohuwar Ministar ne tun ranar Alhamis, a hedikwatar hukumar da ke Abuja, domin yi mata tambayoyi kan badakalar kudaden.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ƙara shiga tsaka mai wuya, Majalisar Dokoki ta dawo da shirin tsige shi

Binciken EFCC ya gano cewa wasu kudin da aka ware don shirin tallafa wa mata na P-Bat Cares for Women Initiative sun shiga aljihun wasu tsirarun mutane da hannun tsohuwar Ministar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng