"Lambarsa Ta Fito": Hukumar EFCC Ta Cafke Tsohon Gwamna kan Badakalar N700bn
- Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya shiga hannun jami'an hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC
- Jami'an na EFCC sun cafke tsohon gwamnan ne kan zargin badaƙalar N700bn a ranar Talata, 4 ga watan Maris 2025
- Wata ƙungiya ta shigar da ƙorafi a kansa kan kuɗin da ya karɓa daga asusun tarayya da yawan basussukan da ya bari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ta'annati da dukiyar ƙasa (EFCC) sun cafke tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.
Jami'an hukumar EFCC sun cafke Udom Emmanuel ne kan badaƙalar N700bn.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta rahoto cewa an cafke tsohon gwamnan ne a ranar Talata, 4 ga watan Maris 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Udom Emmanuel, wanda ya yi gwamna na wa'adi biyu tsakanin 2015 da 2023, ya isa hedkwatar hukumar EFCC ne da misalin ƙarfe 12:30 na rana a ranar Talata.
Tsohon gwamnan ya je hedkwatar ne biyo bayan gayyatar da hukumar ta yi masa, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Meyasa EFCC ta cafke Udom Emmanuel?
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da hurumin yin magana da ƴan jarida ta tabbatar da cafke tsohon gwamnan.
Majiyar ta ce an cafke tsohon gwamnan ne bayan ya amsa gayyatar EFCC domin amsa tambayoyi kan zargin almundahana, karkatar da kuɗi da sata.
"Mun cafke tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kan badaƙalar N700bn."
"Wata ƙungiya mai suna Network Against Corruption and Trafficking ta shigar da ƙorafi a wajen EFCC, wanda hakan ya sanya muka fara gudanar da bincikenmu."
"Masu shigar da ƙorafin sun yi zargin cewa Udom Emmanuel ya karɓi N3trn daga asusun tarayya cikin shekara takwas amma ya bar bashin N500bn da kuɗin kwangila da ba a biya ba waɗanda suka kai N300bn."
"Ana kuma zarginsa da kasa ba da bayani kan yadda N700bn ta yi."
“Udom Emmanuel ya iso ofishinmu da misalin ƙarfe 12:30 na rana sannan daga bisani aka cafke shi."
- Wata majiya
Majiyar ta ƙara da cewa bincike ya bankaɗo yadda aka cire tsabar kuɗi N31bn daga wani asusu mai suna 'ofishin gwamna'.
"Ɓincikenmu ya bankaɗo cire tsabar kuɗi N31bn daga wani asusu guda ɗaya. Sunan asusun ofishin gwamna. An cire tsabar kuɗin ne akai-akai tsakanin 2019 da 2023."
Ba a ji ta bakin hukumar EFCC ba
Ƙoƙarin jin ta bakin daraktan yaɗa labarai na hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ci tura.
Kiran wayar da aka yi masa ya nuna cewa tana a kashe har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
EFCC ta kai tsohon gwamna kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta tasa ƙeyar tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji zuwa kotu.
Hukumar EFCC ta maka tsohon gwamnan a gaban kotu ne tare da ɗansa, Chinedum Orji da waau mutum uku kan badaƙalar N47bn.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng