Sojojin Sama Sun Dura Zamfara, Sun Dauki Alhakin Kai Harin da Ya Kashe Mutane 11
- Hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Hasan Abubakar, ya kai ziyara Zamfara domin jajantawa mutanen da harin bam ya shafa a Maradun
- Harin bam din ya hallaka mutane 11, ciki har da ‘yan sa-kai, yayin da wasu 11 suka jikkata a farmakin da aka yi niyyar kai wa ‘yan ta’adda
- NAF ta dauki alhakin kai harin tare da daukar matakan rage irin wannan kuskure, ciki har da bayar da tallafi da gyara gine-ginen da suka lalace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Babban hafsan rundunar sojin saman Najeriya (NAF), Air Marshal Hasan Abubakar, ya ziyarci wadanda harin bam ya shafa a jihar Zamfara.
A ranar 10 ga Janairun 2025, sojoji suka saki bam a garin Maradun, wanda ya yi silar mutuwar fararen hula da suka hada da ‘yan sa-kai na ZCPG da wasu jami’an tsaro.

Kara karanta wannan
Sojoji da ‘yan ta’adda sun gwabza bayan harin ofishin ‘yan sanda, an samu asarar rayuka

Asali: Twitter
Rundunar sojin sama ta dauki alhakin harin Zamfara
Kabiru Ali, jami’in hulda da jama’a na NAF, ya ce Hasan Abubakar ya bayyana harin a matsayin “abin takaici” da ya saba wa manufar kare ‘yan kasa, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban hafsan ya dauki alhakin faruwar lamarin tare da jaddada aniyar sojojin sama na kare rayuka da rage irin wadannan munanan hadurra.
Ya ce rundunar sojin sama na jin irin radadin da lamarin ya haifarwa mazauna Maradun kuma tana daukar matakin da ya dace don rage radadins.
A cewarsa, mutane 11 da ke cikin rundunar ‘yan sa-kai sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata a harin da aka kai yi niyyar kai wa ‘yan ta’adda.
Yadda sojoji suka samu kuskuren kai hari Zamfara
Da yake bayar da bayanin farmakin, hafsan sojojin ya ce rahotanni tsaro a ranar 11 ga Janairu, sun nuna cewa akwai 'yan ta'adda da ke haye a kan babura suna wucewa ta kauyen Dangebe a karamar hukumar Maradun.
Air Marshal Hasan ya ce:
"Kwana daya kafin ranar, sojoji sun kai farmaki wannan yanki a wani yunkuri na kakkabe 'yan ta'addar da ke biyayya ga Bello Turji, hatsabibin shugaban 'yan bindiga.
"Ci gaba da binciken jiragen leken asiri ya tabbatar da kasancewar wasu ‘yan bindiga dauke da makamai, kuma salon tafiyarsu ya yi daidai da dabarun ‘yan ta’adda da ke aiki a yanki."
Sai dai daga bisani rahotanni suka bayyana cewa akwai fargabar harin ya hallaka wasu ‘yan sa-kai da ke dawowa gida bayan fatattakar ‘yan ta’adda.
Bayan fitar da wadannan rahotanni, hafsan sojin ya ce ya gaggauta tura tawagar bincike don tantance lamarin tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki.
"Binciken ya tabbatar da cewa an kashe 'yan sa kai 11, amma ba da gangan ba, yayin da wasu 11 suka samu raunuka da suka hada da karaya."
- Inji Air Marshal Hasan.
Sojoji sun fadi tallafin da za a ba mutanen Zamfara

Asali: Twitter
Hafsan sojojin saman ya ce za a bayar da tallafin kudi ga iyalan mamatan tare da gyara gine-ginen da suka lalace a harin.
Haka kuma, rundunar za ta samar wa al’ummar garin rijiyar burtsatse da ke amfani da hasken rana don saukaka musu wajen samun ruwa.
Baya ga hakan, rundunar sojin saman Najeriya za ta maye gurbin babura guda biyu da suka lalace a harin da aka kai a yankin.
Air Marshal Hasan Abubakar ya jaddada cewa ko da ba za a iya dawo da rayukan da suka salwanta ba, za a yi kokarin rage radadin da al’ummar ke fuskanta.
Gwamnan Zamfara ya yi wa sojoji godiya
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, wanda ya tarbi rundunar sojin saman, ya nuna godiyarsa bisa wannan ziyara da tallafin sojojin ga wadanda abin ya shafa.
Gwamna Dauda ya bayyanawa iyalan wadanda harin ya shafa matakan da aka dauka domin kaucewa sake faruwar irin wannan iftila’i a nan gaba.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya
A yayin ziyarar, Dauda Lawal ya mika wa rundunar NAF takardar mallakar fili kusa da filin jirgin sama na Gusau don kafa sabon sansanin sojin sama.
Kalli hotunan ziyarar da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X a nan kasa:
Iyalai na neman diyyar wadanda sojoji suka kashe
A wani labarin, mun ruwaito cewa, iyalan kusan mutane 15 da suka rasu tare da wasu tara da suka jikkata a harin jiragen sojin saman Najeriya a Zamfara sun nemi diyya daga gwamnati.
Muhammad Aminu, dan uwan Babangida Ibrahim, daya daga cikin mamatan, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta Zamfara da su biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
An fadada wannan labarin ta hanyar kara bayanin irin taimakon da sojoji ke bukata. Salisu Ibrahim ne ya yi karin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng