Yadda Biden da Amurka Su ka Matsawa Najeriya Lamba, Aka Saki Jami'in Binance

Yadda Biden da Amurka Su ka Matsawa Najeriya Lamba, Aka Saki Jami'in Binance

  • Wani rahoto ya binciko dalilan da suka sa Najeriya ta sassauta shari'ar da ta ke yi da shugaban kamfanin kirifto na Binance
  • Najeriya ta janye tuhumar cin amana da take yi wa Tigran Gambaryan, bisa dalilai na diflomasiyya da kuma tabarbarewar lafiyarsa
  • An kama Gambaryan tare da wani jami’in bisa zargin hada-hadar kuɗi ba bisa ka’ida ba da kuma cutar da tattalin arzikin ƙasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - A ranar 23 ga Oktoba, 2024, gwamnatin Najeriya ta janye zargin manyan laifuffukan da ta ke yi wa Tigran Gambaryan, wani babban jami’in kamfanin Binance da aka kama a watan Fabrairu, 2024.

Ana tuhumarsa tare da kamfaninsa kan laifuffukan da suka hada da zamba, kin biyan haraji, da kuma hada-hadar kudade ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Kisan direbobi: Dattawan Arewa sun yi kaca-kaca da gwamnati da jami’an tsaro

Binance
An bankado rawar da Amurka da taka a shari'ar Shugaban Binance a Najeriya @TigranGambaryan/Bayo Onanuga
Asali: Twitter

A labarin da ya kebanta ga Premium Times ta wallafa, wani lauyan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ya bayyana cewa an janye karar ne bisa dalilai na diflomasiyya da alaka ta kasa da kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa bai yi karin bayani ba, lauyan ya ce raunin lafiyar Gambaryan a tsare ya taka muhimmiyar rawa wajen yanke hukuncin sako shi.

Yadda aka saki jami'in kamfanin Binance

Bayan an sake shi daga kurkukun Kuje, jami’an Amurka da ke Najeriya sun shirya jirgin saman da ya dauke shi zuwa kasarsu ba tare da bata lokaci ba.

Rahotanni sun nuna cewa wannan matakin ya biyo bayan watanni da dama na tattaunawa tsakanin jami’an diflomasiyya na Najeriya da kasar Amurka.

Nadeem
Nadeem ya na daga cikin jami'an Binance da aka kama Hoto: MoreBranches
Asali: Facebook

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa manyan jami’an Amurka, har da tsohon Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden, sun matsa lamba sosai don ganin cewa Gambaryan ya samu ‘yanci.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

An ruwaito cewa Amurka ta yi amfani da rubuta wasiku, kiran waya ba kakkautawa da tarurruka ta yanar gizo domin matsa wa hukumomin Najeriya lamba kan batun sakin Gambaryan.

Dalilin Najeriya na kama shugabannin Binance

An kama Tigran Gambaryan, wanda shi ne shugaban sashen yaki da laifuffukan kudi na Binance, tare da Nadeem Anjarwalla, wanda ke kula da ayyukan Binance a nahiyar Afirka, a ranar 26 ga Fabrairu, 2024.

Ana zarginsu da hana hukumomin tsaro damar binciken yadda kamfanonin hada-hadar kudaden crypto, musamman Binance, ke kawo cikas ga tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta ce Binance ta gudanar da hada-hadar kudi da suka kai kimanin Dala biliyan 21.6 a kasar a shekarar 2023 kadai.

Binance: Najeriya ta sake koma wa kotu

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shigar da sabon ƙara a kan Binance Holdings Limited a gaban babbar kotun tarayya, tana neman kamfanin ya biya diyya ta Dala biliyan 81.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi bayanin yadda bindigogi kusan 4,000 suka bace a karkashin kulawarta

Gwamnatin Najeriya na neman dala biliyan 79 a matsayin diyya saboda asarar da ake zargin Binance ta haifar wa tattalin arzikin ƙasa wajen gudanar da aiki ba bisa ka'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.