Sojoji da ‘Yan Ta’adda Sun Gwabza bayan Harin Ofishin ‘Yan Sanda, An Samu Asarar Rayuka
- Dakarun sojojin Najeriya na Bataliya ta 222 sun hana ‘yan ta’addan ISWAP kai farmaki ga ofishin ‘yan sanda a Malari, jihar Borno
- ‘Yan ta’addan sun yi kokarin sace motar yaki (APC) na ‘yan sanda, amma zaratan dakarun sojoji sun hana su cimma burinsu
- Ba a tantance adadin ‘yan ta’addan da suka mutu ko jikkata ba, amma alamomi sun nuna sun tabbatar da cewa sun yi babbar asara
- Duk da tsananin farmakin ‘yan ta’adda, ba wani jami’in tsaro da ya rasa ransa, sai dai tayoyin motar yaki guda uku sun lalace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Sojojin Operation Hadin Kai sun yi nasara wajen dakile wani mummunan hari da ake zargin ‘yan ta’addan ISWAP sun kai kan ofishin ‘yan sanda na Malari, a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa an yi kiran gaggawa ga hedkwatar rundunar hadin gwiwa ta yankin Arewa maso Gabas (JTF) domin samun agaji yayin da harin ke faruwa.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa harin ya auku da misalin karfe 1:00 na daren ranar Laraba, inda sojojin suka mayar da martani cikin gaggawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun fatattaki 'yan ta’adda
Duk da matsanancin harbe-harbe daga ‘yan ta’addan, sojojin Bataliya ta 222 sun yi kokari wajen kare ofishin ‘yan sanda daga fadawa hannun miyagun.
‘Yan ta’addan sun yi kokarin kwace motocin yaki (APC) mallakin ‘yan sanda, amma sojojin suka hana wannan yunkuri.

Asali: Facebook
Rahotanni sun bayyana cewa ba a tabbatar da adadin ‘yan ta’addan da suka mutu ko suka jikkata ba.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa an ga jini a wuraren da suka bi yayin da suke tserewa daga fagen daga, wanda ke nuna cewa akwai wadanda suka samu raunuka ko suka mutu.

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda sun dura gidan jami'in ɗan sanda a Yobe, sun yiwa ƴaƴansa yankan rago
Sojoji sun tsira daga harin 'yan ta'adda
A gefe guda kuma, babu asarar rai a bangaren jami’an tsaro, wanda hakan ke nuna nasarar da suka samu a wannan fafatawa.
Duk da tsananin farmakin ‘yan ta’adda, babu wani jami’in tsaro da ya rasa ransa, sai dai tayoyin motar yaki guda uku sun lalace.
Bayan nasarar da suka samu, dakarun Operation Hadin Kai sun ci gaba da rike yankin da karfi, domin tabbatar da cewa ba a sake kai irin wannan hari ba.
A baya-bayan nan, hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas sun ragu sosai sakamakon irin kokarin da sojoji da sauran jami’an tsaro ke yi.
Dakarun Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
A baya, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a yaki da ta’addanci bayan sun hallaka kwamandan Boko Haram, Abba Alai, wanda aka fi sani da Amirul Khahid na Alafa.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun kai farmakin ne a cikin hare-haren hadin gwiwa da suka kaddamar a Garin Fallujah da Gwoza, suka ragargaji sansanonin ‘yan ta’adda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng