"Ba Za Mu Yafe ba": Iyalan Wadanda Sojoji Suka Kashe a Zamfara Sun Fara Neman Diyya

"Ba Za Mu Yafe ba": Iyalan Wadanda Sojoji Suka Kashe a Zamfara Sun Fara Neman Diyya

  • Iyalan wadanda harin jiragen saman Najeriya ya rutsa da su a Zamfara sun nemi gwamnatin tarayya da ta jiha ta biya su diyya
  • Iyalan da suka rasa 'yan uwansu a harin, sun nemi a biya diyyar ne sakamakon cewa an kashe 'yan uwansu a taimakawa sojoji
  • Sai dai gwamnatin Zamfara ta yi martani ga wadanda suka nemi diyyar, inda wani hadimin Dauda Lawal ya taka masu burki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Iyalan kimanin mutane 15 da aka kashe da wasu tara da suka jikkata a harin jiragen sojin saman Najeriya a Zamfara sun bukaci diyya daga gwamnati.

An sojoji sun kai hari ranar 11 ga Janairu, 2024, kan wasu mutane a kauyuka da ke Zurmi da Maradun, bisa zaton cewa 'yan ta'adda ce.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Iyalan wadanda sojojin saman Najeriya suka kashe wa 'yan uwa sun nemi diyya daga gwamnati
Zamfara: Iyalan wadanda suka mutu a harin sojojin sama sun nemi diyya daga gwamnati. Hoto: @daudalawal_, @NigAirForce
Asali: Twitter

Zamfara: Sunayen wadanda aka kwantar a asibiti

Wadanda suka jikkata suna karbar magani a asibitin Kaura Namoda, ciki har da jami’in tsaro na jihar, Babangida Ibrahim, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wadanda suka jikkata sun hada da Isa Habibu, Nuhu Usman, Shafi’u Iliyasu da Safiyanu Salisu.

Har ila yau akwai Idrisu Agima, Ukasha Yahuza, Salihu Usman da Nasiru Abubakar 30 na cikin wadanda ke kwance a asibiti.

Iyalan wadanda aka kashe sun nemi diyya

Muhammad Aminu, dan uwa ga Babangida Ibrahim, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara da su biya diyya ga wadanda abin ya shafa.

Aminu ya ce wadanda aka kashe su ne masu rike da iyalansu, don haka wajibi ne gwamnati ta taimaka wa iyalan da suka bari.

Ya kara da cewa:

"Akwai bukatar gwamnati ta dauki nauyin kudin maganin wadanda suka jikkata, kasancewar jami’anta ne suka yi ta'asar."

Ya ce idan gwamnati ta ki biyan diyya, za su bar komai ga Allah, amma ba za su taba yafewa shugabanni ba.

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

Wani mutumi da ya nemi a sakaya sunansa, wanda ya rasa dan uwansa a harin, ya ce akwai gwamnati ta yi biyayya wajen biyan diyya ga iyalan mamatan.

Ya ce rashin daukar mataki zai sa mutane su daina taimaka wa gwamnati wajen yaki da ta’addanci a Najeriya.

Malama Halima Idrisa, matar Idrisu Agima, ta koka kan cewa babu wani tallafi da gwamnati ta kawo bayan wannan mummunan lamarin.

Ta ce sun yi amfani da kudinsu wajen kula da wadanda suka jikkata, don haka suna bukatar gwamnati ta tallafa musu.

Gwamnatin Zamfara ta yi wa iyalan martani

Mustapha Jafaru Kaura, mai bai wa gwamnan Zamfara shawara kan kafofin watsa labarai, ya ce har yanzu ana kan gudanar da bincike.

Kaura ya ce an kafa kwamitoci biyu don gano musabbabin abin da ya faru, daya na gwamnatin jihar, daya na sojojin sama don haka batun biyan diyya bai taso ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Hadimin gwamnan ya ce babu wani mataki da za a dauka ko da kuwa na biyan diyya ne har sai an kammala bincike kamar yadda aka yi a wasu garuruwan a baya.

Kisan farar hula: Sojoji sun ziyarci Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Sama na Najeriya sun aika tawaga zuwa Zamfara don bincike kan harin da ake zargin sun kai wa al’umma bisa kuskure.

Harin ya yi sanadin mutuwar mazauna Tungar Kara inda aka ce tawagar sojojin ta je ta’aziyya da kuma bincike kan yadda aka aikata kuskuren.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.